Wednesday, October 29, 2014

Gwamna Kwankwaso ya kaddamar da aniyarsa ta neman tsayawa takarar shugabancin kasarnan.

Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso
A jiya ne Gwamnan jihar Kano Dr.Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da aniyarsa ta neman tsayawa takarar shugabancin kasarnan a karkashin Inuwar babbar jam'iyar Hammaya ta APC.

Kwankwaso wanda ya yi bikin kaddamawar a babban birnin tarayya Abuja,ya shaida cewa ya samu nasarori da dama da suka zame masa tsani na zama shugaban Kasa a Nijeriya.

Gwamna Kwankwaso ya ce zai amince da yin sulhu tsakanin wadanda suke neman takarar shugabancin Kasarnan a APC, muddin aka bayyana masa sharuddan daya sa za a nemi ya janye takarar tasa.

Tuni dai tsohom mataimakin shugaban kasarnan Atiku Abubakar da Tsohon shugaban kasa Janar Muhammad Buhari mai riyata suka ayyana sha'awar tsayawa takarar shugabancin kasarnan a inuwar jam'iyar ta APC.

A watan gobe ne dai babbar jam'iyar hamayya zata yi zaben fidda gwani, domin tsaida mutum gudada zai tsaya mata takarar shugabancin kasarnan a zaben shekara 2015

Tuesday, September 9, 2014

Maniyata daga Kano za su fara tashi a yau

Kasa mai tsarki
 Kimanin maniyata dari biyar da hamsin ne zasu fara tashi zuwa kasa mai tsarki daga nan jihar Kano.
Jami'in hulda da jama'a na hukumar alhazai ta jihar Alhaji Sani Tanko ya shaida hakan ga manema labarai.

Alhaji Tanko yace maniyatan sun fito ne daga kananan hukumomin Wudil, Warawa, Ajingi, Takai, Albasu da kuma Gaya, wadanda za su tashita jirgin kamfanin Max Air.

Jami'in ya kara da cewa daga cikin jiragen da za su yi jigilar maniyatan sun hada da Max Air, Sky Power da kuma jirgin Kabo.

A cewar Tankon, an jawo lokacin fara jigilar alhazan ne daga Laraba zuwa yau Talata sakamakon kammala shirin fara jigilar da kamfanin Max Air ya yi ,inda alhazan za su tashi da karfe goma na daren yau.

Sunday, September 7, 2014

Dubun wani dan damfara ta cika


          Muhammad Auwal rike da fasfo 2 da takardar fili

Hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa ta'annati wato EFCC ta capke wani Muhammad Auwal da yake gabatar da kansa a matsayin Nasiru Abdulkadir Dantata.

An damke wanda ake zargin ne bayan wani rahoto da aka samu daga sashin kula da filaye na babban birnin tarayya Abuja cewar ya mallaki fili unguwar Maitama dake Abuja dayake mallakin iyalan attajiran nan Dantata.
A yayin bincike an gano cewar wanda ake zargin Muhammad Auwal na da takardun mallakar fili da wasu takardun bogi, haka kuma yana amfani da sunaye biyu da fasfo guda biyu daya da sunan Muhammad Auwal daga jihar Katsina yayin da daya fasfon yake dauke da  suna Nasiru Abdulkadir Dantata daga jihar Kano.

Haka kuma an gano mai laifin yana dauke da takardar shaidar dan asalin karamar hukumar Batsari daga jihar Katsina da suna Haruna Lawal Muhammad.

Masu iya magana dai kance rana dubu ta barawo,rana daya jal ta mai kaya!

Bani da shafin facebook ko twitter- inji San Kano


Mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu
Mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu yace ba shi da shafin twitter ko na facebook.

A wata sanarwa da sarkin yayi wanda sabon dan majen Kano Munir Sanusi ya sanyawa hannu, ya ce duk wani shafi na facebook ko twitter da  aka gani da sunan sa ba na shi ba ne.

Dan haka jama'a su lura!

Friday, September 5, 2014

Za a bude makarantu aranar 22 ga watan Satumba



'Yan makaranta

 A yau ne gwamnatin tarayya ta bada umarnin  a bude makarantun firamare da na sakandire a ranar Litinin 22 ga watan Satumbar da muke ciki.

Hakan ya biyo bayan ganawar da aka yi tsakanin Ministan ilimi Mal. Ibrahim Shekarau da kwamishinonin ilimi na jihohin Kasarnan.

Idan za a iya tunawa an dage komawar makarantun zuwa 13 ga watan Oktoba saboda daukar matakai wajen dakile yaduwar cutar Ebola.

Tuesday, September 2, 2014

Jiya ba yau ba...

Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso

 Kun san 'yan jarida muna yawo muka ci karo da wannan hoto,Gwamnan jihar Kano ne lokacin da yake matashinsa ...

Ibrahim BB Farouk ya rasu

bibi farouk
Marigayi Alhaji Ibrahim BB Farouk
 Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Alhaji Ibrahim BB Farouk ya rasu a jiya a wani asibiti mai zaman kansa anan Kano, yana da shekaru 82 a duniya.

Marigayi BB Farouk ya kasance mataimakin gwamna alokacin shugabancin Abubakar Rimi,na tsawon shekara daya wanda daga bisani aka tsige shi  a shekarar 1980.

Daya daga cikin 'ya'yansa Dr. Farouk BB Farouk ya bada sanarwar  rasuwar mahaifinsa ga manema labarai,inda yace mahaifin nasa ya rasu da misalin karfe 12 na rana.

Kafin rasuwarsa marigayin ya sha fama da mutuwar barin rabin jiki har na tsawon shekaru 10.
An dai haifi marigayi BB Farouk a shekara 1932, ya rasu ya bar matan aure biyu da 'ya'ya 32.

 Daga cikin 'ya'yansa akwai  Dr. Farouk BB Farouk wanda mai baiwa gwamna shawara ne akan karbar baki a fadar gwamnatin Kano.

An dai gudanar da Jana'izarsa a fadar maimartaba  sarkin Kano,yayinda aka binne shi a makabartar kofar mazugal.

Allah ya ji kansa ya gafarta masa...

Friday, August 15, 2014

Likitoci masu neman kwarewa sun yi zanga-zanga


Likitoci masu neman kwarewa sun yi zanga-zanga domin nuna rashin gamsuwarsu bisa matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na korar likitoci kusan dubu goma sha shida a kasarnan.

Likitocin wadanda suka gudanar da zanga-zanga akarkashin kungiyarsu, sun bayyana takaicinsu ga uwar kungiyar likitoci ta kasa a birnin Abuja.

Shugaban kungiyar likitocin masu neman kwarewa Jibril Abdullahi ya yi Allah wadai da matakin da gwamnatin ta dauka na soke koyarda aikin kwarewa akanaikin likita akasarnan.

Da yake karfafa musu gwiwa shugaban kungiyar likitoci ta kasa(NMA)Dr. Kayode Obembe ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta janye kalamanta nadakatar da likitocin.

Masu zanga-zangar daisuna dauke da kwalaye dauke da kalamai daban-daban

Dangote ya bada gudummawar Naira Miliyan 150 domin yaki da cutar Ebola


Aliko Dangote

Attajirin nan Alhaji Aliko Dangote ya bada gudummawar Naira Miliyan 150 domin taimakawa wajen yaki da yaduwar cutar Ebola a Najeriya.

Shugaban gidauniyar Dangote Mrs Ahiambo Odaga ta bada sanarwar a wani zama da akayi da Ministan Lafiya a babban birnin tarayya Abuja.

Madam Odaga ta bayyana cewa Alhaji Aliko Dangote ya yi kira ga ' yan Najeriya da su bada goyon baya  ga  Gwamnatin Tarayya wajen yaki da cutar Ebola inda ya bayyana fatansa na magance Cutar.

Gwamnan Katsina ya auri 'yar Umaru Musa 'Yaradua





        Gwamna Ibrahim Shehu Shema da Amaryarsa Maryam Umaru 'Yaradua

A yau juma'a 15 ga watan Agusta ne  gwamnan jihar Katsina Barista Ibrahim Shehu Shema zai angwance da amaryarsa Maryam 'Yaradua, 'yar fari ga tsohon shugaban kasa marigayi Umaru Musa 'Yaradua.

Za a daura auren ne a sabon masallacin Usmanu Dan Fodio dake birnin na Katsina.

Idan za a iya tunawa Maryam ta taba auren dan sarki Kabir, Badamasi Usman Kabir wanda Allah ya yiwa rasuwa.

Haka kuma kanwarta Nafisa maidaki ce ga  gwamnan jihar Bauchi Isa Yuguda.

Muna taya su murna Allah ya bada zaman lafia, Amin.

Shafin Hatsin Bara ya dawo...

Assalamu alaikum makaranta wannan shafi, ya aka ji da hakuri da mu?.Dafatan anyi azumi lafia kuma anyi bikin sallah karama lafia...Allah ya karbi ibadunmu ya maimaita mana muga na badin ba-da-da lafia.

Wannan shafi na Hatsin bara zai fara da neman afuwarku makaranta...saboda shiru na dan wani lokaci...Amma ina tabbatar muku cewa ya dawo bakin aiki...sai a kasance da shafin.

Wednesday, June 25, 2014

Bam ya tashi a Abuja...


 Rahotanni sun ishe mu cewar da misalin karfe hudu na yammacin yau ne Bam ya tarwatse a rukunin shagunan zamani wato  Emab Plaza dake  kan titin Aminu Kano cresent a Wuse 2,dake babban birnin tarayya Abuja.

Bayanai na nuni da cewa Bam din ya tashi a kofar shiga plazar,kuma akalla mutane shida sun mutu yayin da akalla mutane goma sha biyar suka jikkata..

Ya Ubangiji ka magance mana  wannan Al'amari ka  jikan wadanda suka rasu..

Daliban makarantar koyon aikin tsafta na bukatar gudummawar jininku


Makarantar da Bam ya fashe
Mahukuntan Asibitin Murtala sun yi kira ga Al'umma da su ba da gudummawar jini ga daliban makarantar koyon aikin tsafta wato school of Hygiene da suka jikkata sakamakon tarwatsewar bam a makaranatar aranar Litinin din da ta gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa tuni wasu daga cikin daliban na ta tururuwa asibitin domin bada gudummawar jinin ga abokan karatunsu.

Idan ba a mantaba aranar Litinin din da ta gabata ne bam ya tarwatse a makarantar koyon aikin tsafta dake nan cikin kwaryar birnin Kano inda dalibai 8 suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata.
Daya daga cikin daliban da suka jikkata

A tuna dai na Allah baya yawa baya kadan...

Tuesday, June 24, 2014

Sarkin Kano ya jajantawa wadanda suka jikkata a harin bam din jiya


Sarkin Kano Muhammadu Sanusi 11


A yau ne mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na 11 ya ziyarci wadanda harin Bam  ya rutsa dasu a makarantar koyon aikin duba gari wato School of Hygiene a jiya.

Sarkin ya yi tir da wannan hari tare da kira da a gaggauta  dora wadanda suka samu karaya sakamakon harin. Ya kuma yi ta'aziya ga wadanda suka rasa rayukansu tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.

Rahotanni sun bayyana cewa Wamban Kano Abbas Sanusi da Jarman Kano farfesa Isa Hashim na daga cikin tawagar da suka yiwa sarkin rakiya.

Haka kuma kwamishinan Lafiya ta jiha Dr Abubakar Labaran Yusuf da ta sa tawagar sune suka tari sarkin.

Idan ba a mantaba a jiya ne bam ya fashe a makarantar aikin duba gari wato school of Hygiene,a yayin da dalibai suke tsaka da yin rajistar kakar karatu,inda mutane 9 suka rasa rayukansu sama da mutane 20 suka jikkata.
Maimartaba yana dubiya


Allah ya tsare ya kuma kiyaye gaba...

An Nada sabon waziri a Kano

Sabon Wazirin Kano Sa'ad Shehu Gidado
A ranar Juma'a 20 ga watan Yunin shekarar da muke ciki Sarkin Kano Mhammadu Sanusi 11 ya nada sabon Wazirin Kano.

Waziri Gidado shi ne wand ya maye gurbin sheik Nasir Muhammad Nasir da aka tube bayan marigayi Sarkin Kano Ado Bayero sakamakon rashin amincewar gwamnatin Kano.

Maimartaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu, ya yi kira ga sabon wazirin Kano Sa'adu Shehu Gidado daya baiwa masarautar Kano shawarwarin da suka dace akan al'amuran da suka shafi addini dama walwalar jama'a.

Sarkin wanda ya shaida hakan,yayin bikin  nadin sabon wazirin ,ya bayyana cewa daga cikin muhimman aiyukan shi  sune bada shawarwari a harkokin addinin musulunci da kuma hanyoyin warware matsaloli.

Haka kuma sarki ya yi kira ga sabon waziri da yayi koyi da halayen kwarai na tsohon waziri inda ya yi amfani da mukaminsa wajen dabbaka musulunci da ma jihar Kano.

An haifi Gidado a shekarar 1966 a unguwar Kurawa dake nan Kano.Yayi makarantar Firamare ta Jar kasa daga shekarar 1972 zuwa 1978,daga nan ya tafi makarantar Sakandire ta koyon Arabiya dake Gwale daga shekarar 1980 zuwa 1986. Haka kuma ya yi karatu a makarantar koyon harkar sdhari'a wato Legal daga shekarar 1986 zuwa 1989.

Har ila yau kafin nadinsa Gidado Magatakarda ne a majalisar Masarautar Kano tun a shekara 2001.
Sabon Waziri da ne ga marigayi waziri Shehu Gidado wa ga marigayi Isa Waziri.

Allah ya taya riko...


'Yan Kannywood da dama sun lashe kyautar City people award

Ali Nuhu da Rahama sadau
A jiya ne aka yi bikin bada kyautar jarumta a duniyar Fina-finai da waka na kasashen  Najeriya da Ghana da City people Entertainment suka shirya. 
A yayin da jarumai da dama daga duniyar Kannywood suka samu karramawa.  wasu daga ciki sun hada da:
Ali Nuhu-amatsayin jarumin shekara Nuhu 
Aisha Aliyu Tsamiya -amatsayin jarumar Shekara 
Zahradeen Sani -amatsayin Mataimakin jarumin shekara 
Halima Atete -amatsayin mataimakiyar jaruma ta shekara
Ibrahim Daddy(Kanin miji)-amatsayin sabon jarumi na shekara 

Rahama Sadau(Halwa)-sabuwar jaruma ta shekara 
Abba miko Yakasai-Furodusa na shekara
Maja-Fim din shekara.
Sadik N.Mafiya-Daraktan Shekara
Nazifi Asnanic-mawakin shekara
Mashiryin Fim na shekara-Abba Miko Yakasai

Wednesday, June 18, 2014

Abokan aiki daga wazobia fm da coolfm Lagos.



Abokan aiki daga wazobia fm da cool fm dake Jihar Legos suke cashewa domin  karfafa gwiwar  kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles...dake can a kasar Brazil..

Iyantama ya zama Kaka...


Iyantama da jikalle

Daya daga cikin iyayen Kannywood Lamido Hamisu Iyantama ya zama kaka,'yarsa ta fari  Khadija ta haifa masa jika  Mahmud Hayatu Bako a jiya da safe...

Hamisu  Iyantama ya kasance Jarumi,Furodusa kuma Darakta a duniyar Kannywood  kuma shine mai kamfanin shirya fina-finanai na Iyan tama multimedia da aka kafa tun shekarar 1997. Ga masu neman karin bayani sai su nemi shafinsa akan adireshin www.itmm-iyantama.com

Daga cikin fina-finansa akawai Kilu ta ja bau, dajin so,Kurkuku,Alkawari,Tsintsiya da sauran makamantansu...

Muna adduar Allah ya raya ya kuma dayyaba...

Friday, June 13, 2014

Allah sarki jiya ba yau ba












Wannan hoton gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido(Nabamaina),  a shekarar1979 lokacin yana dan Majalisar Kasa Akarkashin Jam'iyar PRP

Thursday, June 12, 2014

'yan wasan kwallon kafa sun isa kasar Brazil

'Yan wasan super Eagles
Kungiyar kwallon kafa ta super Eagles ta isa kasar Brazil tun shekaran jiya domin halartar gasar cin kofin duniya na bana 2014 da za a fara a yau,inda za su wakilci Najeriya..Ga hotuna da 'yan wasan suka dauka ayayin dirar su kasar..



Muna fatan su dawo mana da Kofi gida...

Sanata Dahiru Awaisu Kuta ya rasu...


Marigayi Dahiru Awaisu Kuta

Sanata Dahiru Awaisu Kuta,wanda dan majalisar dattijai ne mai wakiltar yankin gabashin Jihar Neja ya rasu.
Marigayin mai shekaru 65 a duniya ya kasance mamba daga jam'iyar PDP ,ya kuma  kama aiki amatsayin sanata a ranar 29 ga watan Mayun 2009.

Mu na adduar Allah ya jikan shi ya gafarta masa.

Ahmad Adamu Muazu ya cika shekaru 59 a duniya...

A jiya ne tsohon gwamnan jihar Bauchi  kuma sabon shugaban jam'iyar PDP  Alhaji Ahmad Adamu Muazu  ya cika shekaru 59 a duniya...kuma 'ya'yan jam'iyar suka  shirya  liyafa domin taya shi murna...hotuna daga Jaridar Rariya



Muna yi masa fatan alheri...

Jarumi Sadik Sani Sadik ya zama angwon karni...

Jaririn Sadik Sani Sadik

Mun samu labarin cewa Jarumin Kannywood Sadik Sani Sadik ya samu karuwar da namiji yau da safen nan.

Sadik Sani Sadik da Maijego Murja Shehu Shema
Jarumi Sadik Sani Sadik ya auri Sahibarsa Murja Shehu Shema wacce 'ya ce ga dan uwan gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shehu Shema a ranar 2 ga watan Maris shekara 2013...

Daga cikin fina -finansa akwai Dan Marayan Zaki, Wani Gari, Halacci, 'Yar mama,Addini ko Al'ada ,Sabon Sangaya ,Hanyar Kano da sauran makamantansu.

Muna addua'ar Allah ya raya ,ya baiwa Maijego Lafia ya kuma horewa Baban baby ikon ciyarwa...

Wednesday, June 11, 2014

Allah Sarki ...Jiya ba Yau ba




Garin yawon binciken mu ,muka tsinto wannan hoto,Allah Sarki akwana a tashi yau shekara 26 kenan ana tare Mai martaba Sabon Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi da Mai dakinsa Fulani Sadiya Ado Bayero.


Tuesday, June 10, 2014

Gwamnatin Kano ta nada sabon sarki..


Mai martaba Sarkin Kano Sunusi Lamido Sunusi

A ranar Lahadi 8 ga watan Yunin Shekarar 2014 da ta gabatane aka sanar da sunan  tsohon gwamnan babban bankin Nigeria,kuma Dan buran  Kano Sunusi Lamido Sunusi amatsayin sabon sarkin Kano kuma na 14 a jerin sarakunan fulani..A jiya Litinin 9 ga watan Yunin shekarar 2014 kuma aka mika masa takardar shaidar kasancewa Sarkin Kano
Photo: GOV. KWANKWASO PRESENTS NEW KANO EMIR WITH LETTER OF APPOINTMENT

The new Emir of Kano, Alhaji Sanusi Lamido Sanusi, CON was today (Monday) officially presented with a letter, confirming his appointment, by the governor of Kano state, Gov. Rabi’u Kwankwaso at the Government House in Kano.

Shortly after presenting the letter to the Emir, who is the 14the in the Fulani dynasty of Kano, Governor Kwankwaso, who was full of praise to Allah for making him part of the history, stated that the immediate past CBN governor was appointed based on his sterling qualities and importantly, in view of his lineage as member of the royal family, as required by Kano traditions.
 
His words:”Your appointment into the exalted position of Emir of Kano was guided by our collective and careful judgment of your ability, credibility and capability to provide the required purposeful leadership to enhance the Emirate Council at this crucial period of our history as a state and as a nation”.
 
“The appointment of the Emir is not a political issue. However, we are aware that enemies of the state and of this government have politicised the appointment matter and disseminated misleading information in across section of the media”, leading a political party to start congratulating one of the contenders for the exalted position, before the official announcement, he added.
 
Governor Kwankwaso explained that the committee of Kano King Makers presented a list of three nominees to the governmental required by law and tradition, and after due consultation and consideration of all variables, the one destined by Allah to become Emir (Sanusi Lamido), was eventually selected.
 
Consequently, he appealed to traditional leaders as well as the generality of the people in the state to accept the new Emir as the will of Allah and support him towards moving Kano forward. He also warned those inciting youths to protest the appointment of the Emir to desist from doing so as it is not in the best interest of anybody in the state.
 
The governor advised Emir Sanusi Lamido, a grandson of the late Emir Sanusi Bayero, the 11th Emir of Kano under the Fulani dynasty, to be a father to all and to be just and fair in dealing with his subjects, as exemplified by his forefathers.
 
The governor, who paid glowing tribute to late Emir Ado Bayero, said a befitting house has since been constructed for his family at Sharada area of Kano city, adding that government would do its best to ensure that they continue live as comfortable as possible.
 
Responding, Emir Sanusi Lamido promised to rule according to the tenets of Islam, urging all other contenders for the throne and other members of the ruling family to, as a family, continue to live in peace and harmony. He promised to carry everybody along to make his tenure eventful.
 
The emir expressed gratitude to Almighty Allah for choosing him to rule Kano state as the 14th emir and thanked the governor, the Kano kingmakers and all others that made the appointment possible.
 
All the Kano King makers, namely, Madakin Kano, Alhaji Yusuf Nabahani Cigari Ibrahim, Makaman Kano, Alhaji Abdullahi Sarki Ibrahim, Sarkin Dawaki Maituta, Alhaji Bello Abubakar, the Sarkin Bai, Alhaji Mukhtari Adnan and the Senior Councilor of the Emirate Council, Wamban Kano Alhaji Abbas Sanusi attended the ceremony.
 
Other personalities who witnessed the well attended event are the Walin Kano, Alhaji Mahe Bashir, Senator Kabiru Gaya and APC chieftain, Malam Nasiru el-Rufa’i.
 
Halilu Ibrahim Dantiye, fnge, mni
Director of Press and Public Relations
to the Executive Governor of Kano state
9/6/2014

Photo: Gov. Rabi'u Musa Kwankwaso the new Emir of Kano, His Highness Sanusi Lamido Sanusi in a tete-a-tete during the formal presentation of letter of appointment to the latter by the former at Africa House, Government House, Kano, today, Monday. Photo: Govt. House, Kano. 9/6/2014

Allah ya taya Mai Martaba riko...

Friday, June 6, 2014

Masarautar jihar Gombe ta nada sabon Sarki..

Photo: Allah taya ka riko.amin.sarkin gombe na sha daya.
Sabon Sarki Abubakar  Shehu  Abubakar

A yayin da  jihar Kano ta ke alhinin rasuwar Mai Martaba sarkin Kano Alhaji Ado Bayero a safiyar yau, A bangaren guda Masarutar jihar Gombe ta nada sabon sarkinta Abubakar Shehu Abubakar,bayan rasuwar Mahaifinsa Sarki  Shehu Usman Abubakar daya rasu a makon da ya gabata.

Sabon Sarki Abubarkar Shehu Abubakar dan shekaru 36 a duniya,ya Kasance karami daga cikin 'ya'yan sarki..kazalika shi ne sarkin Gombe na 11.

Muna taya shi fatan alheri, Allah ya taya shi riko...

SAN Kano ya rasu...

Mai martaba SAN Kano Alhaji Ado Bayero


Da sanyin safiyar yau Juma'a 6 ga watan Yunin shekara 2014 ne rahotanni suka ishe mu cewa Allah ya yi wa  Mai Martaba sarkin Kano Alhaji Ado Bayero rasuwa bayan ya sha fama da rashin lafia. Za  a yi Jana'izarsa bayan da misalin karfe hudu na yamma,in da ake saran za a binne shi a makabartar Masarautar dake gidan sarki na unguwar Nassarawa

An Haifi Mai martaba Alhaji Ado Bayero a ranar 25 ga watan Yulin shekarar 1930,ya hau karagar mulki a shekara ta 1963 yana da shekara 33 a duniya , kuma ya kasance Sarkin Kano na 13 karkashin tutar fulani. Mai martaba Alhaji Ado ya kasance da  ga sarkin Kano Abdullahi Bayero kuma jikan Sarkin Kano Muhammad Abbas.

Dr.Ado Bayero ya riki mukamin jakadan kasar Sinigal,inda daga nan ne ya dare karagar mulki.

Ashekarar da ta gabata ne wasu  masu tada kayar baya suka kai wa tawagar Sarkin ayayin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga bikin saukar Alqur'ani acikin birnin Kano.Kafin bikin cikarsa shekaru 50 akan karagar mulki.

Mai martaba Sarkin Kano ya rasu yana da shekaru 84 a duniya. Ya bar 'ya'ya 62, maza 30 mata 32.

Allah ya jikan sa ya gafarta masa,Yasa Aljanna makoma...

Friday, May 30, 2014

Saima Muhammad ta zama Amarya!!



Jaruma Saima da Angonta
A gobe Asarbar ne 31 ga watan Mayun shekara 2014 za a daura auren Jarumar kannywood Saima Muhammad ,A unguwar Gama, Brigade cikin birnin Kano da  Misalin Karfe sha daya  na safe.

Idan ba a manta ba Saima na daga cikin  jaruman sahun farko na  Kannywood,daga cikin fina-finan ta akwai Kilu ta ja bau wanda shi ne fim dinta na farko da aka yi a shekara 1996 zuwa 1997 da Kamfani Iyantama Multimedia suka shirya,sai  Iyaka, 'Yanmata,Mumbari, Khushu'i da Zuri'a da sauran makamatansu.

Ko kun san cewa fim din kilu ta ja bau shi ne  fim din da ya fara jan hankalin 'yan mata da samari shiga harkar fim? Saima ta fito da sunan Aina'u a fim din,Kuma fim din ya yi kasuwa...

Muna yi mata fatan alheri...

Thursday, May 29, 2014

A duk sa'ilin da ka yi fushi ka yi asarar farin ciki na sakan 60!!

Abokan aiki kenan daga Tashar mu ta Coolfm da Wazobiafm dake Jihar Legas suke kayatar da masu karanta wannan shafi, Shugaban Rukunin Tashoshin Amin Mousalli shi ne akan tebir...

Ka ziyarce mu idan har ka baiwa farin ciki muhimmanci!!!

Speta janar ya kusa zama angon karni...




M.D Abubakar da Zahra
Kun san mu ba ma rabo da tsegumi, rahotanni sun ishe mu cewa speta janar din 'yan sandan kasarnan Muhammad Dikko Abubakar ya ku san zama angon karni.

Idan ba ku manta ba Speta janar din ya sake aure a watan Satumbar shekarar 2013 bayan mutuwar matarsa Maryam Abubakar a watan Jinairun shekara 2012.

M.D Abubakar ya auri Zahra Bunu, 'ya ga tsohon jakadan kasar Faransa a shekara 1999 Alh Bunu Sheriff Musa.

Speta janar mai shekaru 54 da Amaryarsa Zahra mai shekaru 36 zasu dansu na fari nan ba da dadewa ba.

Muna addu'ar Allah ya raba lafiya.... 

Wednesday, May 28, 2014

Sarkin Gombe ya kwanta dama...



Marigayi Sarkin Gombe Alh Dr.Shehu Abubakar
 A yammacin jiya ne  muka samu rahoton rasuwar sarkinGombe Alh Dr.Shehu Abubakar,wanda ya rasu a jiya a wani asibiti dake kasar Ingila, bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Sakataren gwamnatin jihar Gombe Abubakar Bage ya bada tabbacin rasuwar acikin wata sanarwa da ya fitar.

Rahotanni sun bayyana cewa a yau ne ake sa ran dawo da gawar marigayin gida Najeriya domin sitirta ta.

Kafin rasuwarsa,Sarki Gomben shugaban majalisar  saurautun gargajiya  na jihar Gombe tun shekarar 1984.

Allah ya jikansa ya gafarta masa..

Monday, May 26, 2014

Abin ya zo...in ji mai tsoron wanka!


Jaruma Hadiza Gabon
Rahotanni sun ishe mu cewa shahararriyar jarumar Kannywood Hadiza Aliyu wacce aka fi sani da Hadiza Gabon za ta shiga daga ciki...Ana sa ran daura auren a ranar Juma'a 30 ga watan da muke ciki.

Jaruma Hadiza Gabon  ta  shiga  harkar fim a shekarar 2009,daga cikin fina-finanta akwai 'Yar maye, Zaman Take, Badi ba rai, Basaja,Daga ni sai ke, Babbar Yarinya da sauran makamantansu.

Mu na yiwa amaryar nan da kwana uku fatan alheri!!

Tuesday, May 20, 2014

Furodusa Musa Jalingo Ya kwanta dama



Photo: Furodusa Musa Jalingo Ya Rasu

Allah yayi wa Musa Jalingo rasuwa yau 17th May 2014 Musa jalingo dai yana daya daga cikin manyan furodusoshin masana'antar fim, kuma jarumi.
Za a yi Jana'izarsa a gidansa dake Sabuwar Gandu. Allah ya gafarta masa yasa ya huta amin! Shine kuma mai kamfanin Kajal Films Production.

Musa Jalingo shine sanye da jar shadda daga dama.
Marigayi Musa Jalingo shi ne sanye da jar shadda


Rahotanni sun ishe  mu cewa daya daga cikin Manyan Furodusoshin Kannywood Musa Muhammad Jalingo ya rasu bayan rashin lafiya da ya sha fama .An yi jana'izarsa tun ranar juma'a 15 ga watan Mayun shekarar 2014 a gidansa dake Sabuwar Gandu cikin birnin Kano.

Kafin rasuwarsa, shine yake da kamfanin shirya fina-finai na Kajal,kuma yakan fito a fina-finan Kannywood amatsayin jarumi. Daga cikin fina-finansa akwai Alawiyya, Ciki daya, Giwar mata, Tsananin so da sauran sauransu.

Ya rasu yabar mace daya da 'ya'ya hudu. Allah ya ji kansa ya gafarta masa... 








Wednesday, May 14, 2014

Bikin ranar yara....

Ina yara Manyan gobe? ga ranar ku nan...Iyaye ku kai 'ya'yan ku kada ku bari a baku labari

Maryam Mushaqqa ta koma dakinta...


Jaruma Maryam

Jarumar Duniyar Kannywood Maryam ta koma dakinta...Rahotanni sun bayyana cewa jarumar ta koma harkar fim bayan mutuwar auren...saidai kuma da yake zaman bai kare ba maigidan ta ya yi bikon matarsa kuma har ta koma dakinta wajen mijinta da 'ya'yanta hudu a kasar Kamaru
.
Daya daga cikin fina-finan ta shi ne Sarmadam wanda suka yi ita da marigayi Ahmad S.Nuhu.

Mu anan mu na yi mata fatan alheri kuma Allah yasa mutu ka raba..

Monday, May 5, 2014

Allah sarki...Akwana a tashi...

Marigayi Umaru Musa Yar'adua

A rana irin ta yau 5 ga watan Mayu shekara 2010 shugaban kasa Umaru Musa Yar'adua ya kwanta dama sakamakon rashin lafiya da ya sha fama.

Kafin rasuwarsa,shi ne shugaban kasar Najeriya  na 13,Ya kuma rike mukamin gwamnan jihar Katsina daga  29 ga watan Mayu shekara 1999 zuwa 29 ga watan Mayu shekara 2007.

Shi ne ya lashe zaben Shugaban kasa mai cike- da kace-nace karkashin Jam'iyar PDP da aka gudanar a 21 ga watan Afrilu kuma aka rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu shekara 2007
.
A Shekara 2009 Ya bar gida Najeriya zuwa Kasar Saudiya domin duba lafiyarsa abisa matsalar da ta shafi Koda.
A ranar 24 ga watan Fabrairu 2010 ya dawo gida Najeriya bayan ya sha fama da jinya ,inda ya rasu a ranar 5 ga watan Mayu,A ka kuma binne shi aranar 6 ga watan Mayu  a Unguwar Yar'adua.
Ya rasu ya bar Mata daya da 'ya'ya takwas...

 Yau shekaru hudu kenan da ya bar duniya...Allah ya jikansa ya gafarta masa...