Tuesday, December 24, 2013

Hoton mu na yau





Ali Nuhu da Adam Zango shi kuma dayan kowaye?
Photo: Chairman,my prince and I
Adam Zango da Ibro da kuma Ali Nuhu



Saturday, December 21, 2013

An karrama wasu 'yan kannywood a PAMSA 2013



Daga hagu:Van V. Jackie,Stella, Yakubu, Sani da Adam
 Mujallar Papyrus ta gudanar da taron bayar da lambar yabo ga 'yan  duniyar fim na Kannywood tare da takwararta na Nollywood da aka gabatar a Otal din Sheraton dake babban birnin tarayya Abuja.

Taron da aka yiwa lakani da PAMSA 2013 ya samu halartar jarumai irin su Sani Danja, Yakubu Muhammad ,Ibrahim Mai shinku,Jamila Nagudu, Adam A Zango da sauransu daga bangaren Nollywood akwai Jackie Appiah,Desmond Elliot, Ramsey Noah, Van Vicker ,Stella Damasus da sauransu.

Wasu da aka karrama sun hada dai:
Jamila Nagudu-gwarzuwar jaruma 2013
Adam A.Zango-gwarzon jarumi 2013
Yakubu Muhammad-gwarzon mai bada umarni 2013

Friday, December 20, 2013

Fati Ladan ta zama amarya!

Yarima da Fati

 Ina masoyan shahararriyar 'yar fim din Hausan nan Fati Ladan?...to albishirunku jarumar ku ta zama amarya yau  da angon ta Yarima Shettima...mun ji ance wai mai kare hakkin bil adama ne.

Ga wadanda suke so su tabbatar da zance na , yau da daddare akwai walimar cin abinci a  Otal din Royal Tropicana amma fa na garin Kaduna!.
Soyayya ruwan zuma!
Jarumar ta ce tana neman gafararku...masoyanta da abokanan aikin ta...
Mu anan mu na taya Fati murna Allah ya ba da zaman Lafia!!!

A sha sauti lafia...

                                    Wakar Sani Danja mai taken Ruwa Guba, A sha sauti lafia

Ta faru ta kare...

Photo: Gov. Rabi'u Musa Kwankwaso of Kano state signing the Kano State Street Begging Prohibition Law at the venue of the mass wedding of 1,111 today, Thursday. Also in the picture are the Emir of Ningi, Alhaji Yunusa Mohammed Danyaya, who represented the Sultan of Sokoto, the Wamban Kano, Alhaji Abbas Sanusi, who represented the emir of Kano, Alhaji Ado Bayero and the Deputy Gov, Dr, Abdullah Ganduje among others. Photo: Govt. House, Kano. 19/12/2013.







Gwamna Kwankwaso yana rattaba hannu akan dokar hana bara
 A Jiya ne gwamnan jihar Kano Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso ya rattaba hannu akan dokar hana barace-barace a jihar, gwamnan ya sanya hannun ne a fadar gwamnati bayan bikin aurar da amare dubu daya da dari daya da goma sha daya.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne mabarata suka yi dandazo akofar majalisar jihar domin nuna rashin amincewarsu a kan dokar.

Sai dai kuma gwamnan ya yi musu albishir da cewa zai bada mukaman gwamnati ga wadanda suka cancanta, saura kuma za a rinka basu albashin dubu goma duk wata.

Kano ta sake aurar da wani rukunin zawarawa...






https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEiRjUGAyMuej9VTnWTwIqyRu00_mOKqxeNlcICspJ6Pm1BvwRDbRL-C7qBtvxhZezRQROEOxEhApECAO6jLv_7jxp2IlJvtpj0uH8cgUql3pgaKmVNJF57RlhMNv1FfXgle0YNjqyg5-Sgd/s1600/1.jpg
Jerin wasu amare da angwaye


A jiya  ne gwamnatin Kano ta sake aurar da wasu rukunin zawarawa har da 'yanmata karo na hudu, inda ta aurar da dubu daya da dari daya da goma sha daya, sittin daga ciki mabiya addinin kirista ne.

Kamar yadda al'adar shirin yake an bai wa kowacce amarya tagomashin dubu ashirin lakadan amatsayin jari sa'annan kamfanin yahuza suya ya gwangwaje kowacce amarya da kullin murgujejiyar kaza.


Rahotanni sun bayyana cewa an akashe akalla Naira miliyan dari biyu da saba'in da takwas wajen bikin auren.


Kayan dakin da aka baiwa kowacce amarya

Thursday, December 19, 2013

Daliban jhar kano a kasar Malaysia

https://fbcdn-sphotos-a-a.akamaihd.net/hphotos-ak-prn1/1532040_550349548388840_1182680109_n.jpg
Daliban jihar kano a kasar malaysia


Dalibai 'yan asalin jihar Kano da gwamnatin jihar ta tura karatun Harshen Turanci A kasar malaysia .

Kwankwaso da direbobin jiragen sama in Allah ya yarda


Gwamna Kwankwaso da tawagarsa tare da dalibai na makarantar koyon tukin jirgin sama a kasar Jordan
 Jerin dalibai 'yan asalin jihar Kano da gwamnatin jihar karkashin shugabanci  Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ta tura kasar Jordan domin karatun koyon tukin jirgin sama.

Wednesday, December 18, 2013

Qa-qa-qara-qa-qa...an raba rana tsakanin jam'iyar PDP da APC a majalisa



'Yan majalisa 37 ne daga cikin 208 'yan Jam'iyar PDP suka tattara komatsansu zuwa jam'iyar 'yan maja ta APC.

Canjin shekar na kunshe ne cikin wasikar da kakakin majalisar Aminu Tambuwal ya gabatarwa manema labarai a yau din nan.

'Yan majalisar da suka canja shekar sun bayyana cewa sun yanke shawarar yin hakan ne saboda rarrabuwar kanu da wutar rikici da ta kama a cikin jam'iyar tasu ta PDP.

Hausawa dai kan ce ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare!!!


Ba a rabu da Bukar ba...




A yayin da ake murna, kungiyar malaman jami'a  na ASUU ta janye yajin aiki na tsawon wata biyar da ta shafe tana yi...kwatsam kuma sai kungiyar likitoci ta kasa ta yi shelar tafia yajin aikin jan kunne na kwana biyar...su ma dai korafin su bai wuce gazawar gwamnatin tarrayya na biya musu bukatunsu ba. Ya Allah gamu gareka.

 Wannan shi ne ba kafa ba ...cinyar baya, ana dara ga dare ya yi.


Sannu -sannu ba ta hana zuwa...


                                                  Ameen Khan da Ponam Pandey

Ameen Khan-Kano haifaffen dan Kano ne wanda ya ke kokarin nemawa kansa mazauni a duniyar fina-finan india, kuma ya yake da burin  ya shahara kamar jarumin indian nan Shahrukh Khan, kuma mai muradin kawo manyan 'yan fim din india zuwa Najeriya tare da kokarin kulla dangantaka tsakanin 'yan Bollywood da Kannywood.
Masu iya magana dai kan ce...sannu-sannu bata hana zuwa..sai dai a dade ba a je ba...!!!


Tuesday, December 17, 2013

Nafisa Abdullahi ta musanta rade-radin ta yi hannun riga da duniyar Kannywood



Nafisa Abdullahi
Shahararriyar 'yar fim din nan Nafisa Abdullahi wacce ta zamo gwarzuwar jaruma ta bana a bikin Kannywood na kamfanin MTN  ta musanta rade-radin da ake na cewa ta yi hannun riga da duniyar Kannywood. Nafisa ta shaida hakan ne a jaridar Rariya.

Idan ba a manta ba, a kwanan baya ne kungiyar Afman ta dakatar da jarumar daga yin fim har na tsawon shekara biyu wanda kuma daga bisani aka sulhunta suka janye hukuncin da aka dauka a kanta.

Nafisa dai ta yi fina-finan Hausa da dama irinsu: Mudubin Dubawa, Sai wata Rana, Dan marayan Zaki, Ban sake ta ba, Abin sirri ne,Gabar cikin gida,Addini ko Al'ada da sauransu...kuma tana kanyi...

Dan haka, ina masoyan jaruma Nafisa... ta na nan daram a duniyar Kannywood!

Hoton mu na yau...

Photo
Sani Danja da iyalensa

T.Y Shaba ya zama angwan karni...



T.Y Shaba da jaririyarsa
Shahararren mawakin hausan nan kuma furodusa na fim din hausa T.Y Shaba ya samu karuwa na santaleliyar jaririya jiya da daddare.

Muna addua Allah ya raya,ya baiwa maijego lafiar shayarwa, ya kuma baiwa baban baby ikon ciyarwa...sai mun zo suna!

Maijego Samira Ahmad  da TY. Shaba da kuma jaririya

Daliban Jami'a ina kuke?



Daliban jami'a

A jiya ne kungiyar malaman jami'a na ASUU suka janye yajin aikin tsawon wata  biyar, kungiyar ta janye yajin aikin ne bayan da aka cimma matsaya tsakaninta da gwamnatin tarayya, wanda shugaban kungiyar kwadago Comrade Abdulwaheed Omar ya wakilci gwamnatin tarayyar...an yi zaman sulhun ne a jami'ar fasaha na garin minnan jihar Neja.

Dan haka daliban jami'a sai  a tattara komatsai a koma makaranta...haka Allah yaso da ku, ku da baku da gatan karatu a kasashen waje!!

Jiya ba yau ba...




Janar Muhammadu Buhari

Allah sarki jiya ba yau ba... yau din nan ne Janar Muhammadu Buhari ya cika shekara  71 a duniya.
Mu na rokon Allah ya kara lafia...ya kuma cika burinka na alheri.

Monday, December 16, 2013

Ba kwa jifan mu shiyasa muke sata...inji Rotimi


Gwamnan jihar Ribas Rotimi Amaechi
Jama' a kuna ji kuwa!! Gwamnan jihar ribas Rotimi Amaechi ya shaida cewa abin da yasa 'yan siyasa suke wawure dukiyar jama'a, shi ne saboda 'yan kasa sun zuba musu na mujiya basa jifansu.

Mr Amaechi ya bayyana hakan ne a wani taron tunawa da marigayi Nelson Mandela da aka gudanar a jihar legos.
 Ya kuma kara da cewa da 'yan Najeriya za su yi zuciya  sun rinka jifan barayin gwamnati da yanzu labari ya sha bam-bam domin ganin cikkaken bidiyo shiga ireporters tv

'yan Najeriya kalubale gareku...idan kun ga barayin gwamnati ku jefesu..amma fa ba a baki na ba...Gwamna Rotimi ya fada!!!

Kisan-gillar da aka yi wa wani mutum a garin Kaduna.

Sifeton Janar na 'yansandan Najeriya , Muhammad D.Abubakar




A ranar Asabar din  da ta gabata ne mazauna layin Aminu da ke kusa da tsohon cocin YMCA a Tudun Wada Kaduna suka wayi gari cikin tashin hankali saboda samun gawar wani mutum mai suna Musa Aliyu da ke gidan kallo an masa yankar rago.
Mutumin wanda ya jima yana harkar gidan kallon kwallo babu wanda ya san ko su wane ne suka yi masa wannan kisar gilla, illa makwabta sun wayi ne suka tarar da gawarsa a kwance a bakin shagonsa cikin jini.
Wasu da suka ga gawar sun shaida wa manema labarai cewa an sassare shi kafin aka yi masa yankan rago.
Akwai masu zargin wani yaronsa da ke duba masa shago da kashe shi, kasancewar tare suke kwana a shagon. An ce tun daga ranar da abin ya faru babu wanda ya san inda yaron yake.

Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ne ya kawo yaron amma babu wanda ya san daga ina ya kawo shi. Tare kuma da yaron suke kwana a cikin shagon har zuwa lokacin da abin ya faru. Sai dai har yanzu ba a ga yaron ba.

Marigayi Musa ya taba yin aure har yana da da daya, amma wasu sun ce sun rabu da matarsa shi ya sa ya koma kwanan shago a inda yake harkar nuna kwallo.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, DSP Aminu Lawan ya ce sun fara bincike domin gano abin da ya faru a ranar.
Masu iya magana dai kance idan ajali yayi kira ko ba ciwo sai anje...

Ba a nakasashshe sai kasashshe...


Ibrahim yana kirga kudi da yatsun kafa.
















Ibrahim Amadu,dan shekaru 27 wanda dan asalin kauyen Kargo ne da ke cikin karamar Hukumar Sumaila ta jihar Kano da ke yawon bara a jihar Legas, ya shaida wa manema labarai cewa da yatsun kafarsa yake yin komai.inda yace ba abin da ba ya iya yi da yatsun kafarsa." Ina kirga kudi da su, ina ma’amala da wayar salula, don ina iya buga waya ina kuma iya amsawa. Ina yin gare-gare na yara da motar kara ta yaran kauye. Kuma da kaina nake gyaran janaretona idan ya samu matsala, ina sanya kaya. Ina yin abubuwa da yawa ba tare da an taimaka mini ba". 

Sai dai kuma ya bayyana cewa, ‘Akwai abubuwan da ba zan iya yi da kaina ba sai an taimaka mini, kamar wanka da wanke bahaya, wani lokaci ma sanya kaya yana yi mini wahala sai an taimaka mini. Ka san yadda rayuwa take ko wanda yake da hannaye biyu ma ba komai yake iya yi da kansa ba, wata rana sai ya nemi taimakon jama’a a wani abu. ya kuma gode wa Allah da Ya ba shi  damar yin wadansu abubuwa da yatsun kafarsa, yana fatan Allah Ya yi masa sakayya da gidan aljanna sakamakon wannan lalura da Allah Ya dora masa.’
Ya ci gaba da bayyanin cewa haka Allah ya halicce shi babu hannuwa biyu, amma  lafiyarsa kalau, don har matar aure yake da ita a garinsu.
Ya ce dole ce ta sanya yake barace-barace a kan titin Legas don ba shi da jarin da zai gudanar da harkar kasuwanci.
Ibrahim ya kara da cewa, zai daina yawon bara a Legas idan da zai samun tallafi daga ’yan siyasa da gwamnatoci.

 "Har wajen dan majalisarmu na je mai suna Kawu Sumaila don ya taimaka mini ya ba ni jari na bude shagon sayar da kaya amma sai ya ce na je garinmu na samu Sani Ahmed, da na je wurin Sani  ban samu komai ba, sai kawai na yanke shawarar na zo Legas na cigaba da bara don na samu jarin da zan fara sana’a a Kano".
Ibrahim ya kara da cewa" ko yanzu na samu tallafin jari da zan bude sana’ar saye da sayarwa zan bar bara na koma gida Kano"

Hausawa dai kan ce ba a maraya...sai rago

Monday, December 2, 2013

Yadda ranar Cool/wazobia fm ta kasance a filin bajakole

A ranar asabar din da ta gabata ne gidan rediyon cool da wazobia suka gwangwaje masoyansu a bikin bajakolen da ake gudanarwa a cikin Kano.Ga yadda ranar ta kasance cikin hotuna.....
Mohd Habu Sule na sashin tallace-tallace na gidan rediyo cool da wazobia
Lt.John,Ladygwen,chiboi,Asmau,Sisiwazibia
Sisi Wazobia na cashewa

daga dama Kay,Sophie ,Yasmin,Gymnastic,Babs,Beebah da Moblaze

Kiyara da Hayan masu shirin yara a coolfm

Joey da Dj Minister

Gymnasatic na Wazobia
Mina Indiana,Babs,Kiyara ,Hayan,Beebah da Chiboi


Chiboi da daliban Queen Sci.Academy 'yargaya da suka kawo ziyara  rumfar coolfm
Chiboi da 'yanmatan coolfm
Lt .John da Dj Minister
Wasu daga cikin masoya gidan rediyon
 
daga hagu Lady gwen,Beebah,Yasmin da Sophie

Rumfar cool/wazobia a filin bajakole

Friday, November 29, 2013

Sani Danja a taron hukumar musayar kudade a Abuja

Photo
Shugaban hukumar musayar kudade ta kasa tare da takwaranta na kasar Brazil su na dansewa da Sani Danja

Photo
yayin tattaunawa
Photo
Sani Danja da Emeka Ike da sauran 'yan wasan Nollywood

Wednesday, November 27, 2013

Motar 'yan maja ta APC ta debi 'yan 7.



Usmanddm Usman's photo.
Jam'iyar APC ta 'yan Maja
A jiya ne , kwastam  kafofin yada labarai suka kwaza cewa gwamnonin jihohi bakwai  na jami'yar PDP da aka fi sani da "yan bakwai" sun yi tsallen albarka sun koma  sabuwar jamiyar adawa ta APC.

Hakan ya biyo bayan taron da bangarorin biyu(jam'iyar APC da gwamnonin 7) suka gudanar a Abuja,in da suka daura damarar kalubalanta tare da baiwa  jam'iyar PDP mai mulki kashi a zaben 2015.

Gwamnonin da suka balle dai su ne gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, gwamnan Ribas, Rotimi Amechi, gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako, gwamnan Jigawa, Sule Lamido, gwamnan Kwara, Abdulfatah Ahmed, da gwamnan Niger, Muazu Babangida Aliyu.

Saidai kuma zaune bata kare ba domin kuwa kakakin gwamnan Niger, Danladi Ndayebo, ya ce har yanzu gwamnan jihar Muazu Babangida Aliyu da takwaransa na jihar Jigawa Sule Lamido su na cikin jam'iyyar PDP daram.
Gwamnoni 'yan bakwai
.

Tuesday, November 26, 2013

Yadda bikin Kannywood ya kasance.

Ali Nuhu da Moblaze na coolfm
Ali Nuhu na kayatar da baki
Babs da Beebah na coolfm
Ishaq sidi Ishaq,da Iyan tama tare da mataimakin gwamna Abdullahi Umar Ganduje
Dr Abdullahi Umar Ganduje lokacin da yake jawabi
Gwamnan jihar Kaduna Alh Ramalan Yaro
Jerin manyan baki da suka halarci bikin
Sani Danja

A Ranar Asabar din da ta gabata ne aka gudanar da bikin bada kyaututtuka na Kannywood karo na farko da kamfanin sadarwa na MTN ya dauki nauyi. Bikin ya samu halartar mataimakin gwamna Dr Abdullahi umar Ganduje, gwamnan jihar Kaduna Alh Ramalan Yaro da Hakimin Dala Alh Aminu Ado da kuma masu ruwa da tsaki a harkar fina-finan kannywood. Daga cikin wadanda  bai wa kyaututtuka akwai Ali Nuhu, Nafisa Abdullahi, Sani Danja, Aminu Saira, Yakubu Muhammad, Zaharaddeen Sani ,Adam Zango dasauransu.Ga kuma hotuna na daga abin da ya samu a bikin domin kashe kwarkwatar idanunku.

Monday, November 25, 2013

A sha sauti lafia...



download
Sani Danger da Terry G -

                           http://www.hulkshare.com/9japride/sani-danja-ft-terry-g-basu-iyawa


                       Wakar sani danja da aka kaddamar ranar asabar din da ta gabata...ayi sauraro lafia.

Wednesday, November 20, 2013

Ziyarar Kwankwaso a kasar Jordan

Gwamna Kwankwaso tare da daliba Halima
Kwankwaso na tattaunawa da jami'an jami'ar kimiyya ta kasar Jordan
Gwamna Kwankwaso tare da mukarrabansa da kuma dalibai 'yan jihar Kano masu karatun digiri na biyu a kasar Jordan







Kunnenku nawa?!

Mawaki Terry G da Sani Danja
Ina masoyan mawakin nan kuma shahararren dan wasan Hausa Sani Danja? Gwanin na ku zai fito mu ku da sabuwar wakarsa wacce ya yi da mawakin kudun nan Terry G mai suna "Basu Iyawa" za a saki wannan waka a ranar 23 na watan nan da muke ciki..