Friday, November 29, 2013

Sani Danja a taron hukumar musayar kudade a Abuja

Photo
Shugaban hukumar musayar kudade ta kasa tare da takwaranta na kasar Brazil su na dansewa da Sani Danja

Photo
yayin tattaunawa
Photo
Sani Danja da Emeka Ike da sauran 'yan wasan Nollywood

Wednesday, November 27, 2013

Motar 'yan maja ta APC ta debi 'yan 7.



Usmanddm Usman's photo.
Jam'iyar APC ta 'yan Maja
A jiya ne , kwastam  kafofin yada labarai suka kwaza cewa gwamnonin jihohi bakwai  na jami'yar PDP da aka fi sani da "yan bakwai" sun yi tsallen albarka sun koma  sabuwar jamiyar adawa ta APC.

Hakan ya biyo bayan taron da bangarorin biyu(jam'iyar APC da gwamnonin 7) suka gudanar a Abuja,in da suka daura damarar kalubalanta tare da baiwa  jam'iyar PDP mai mulki kashi a zaben 2015.

Gwamnonin da suka balle dai su ne gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, gwamnan Ribas, Rotimi Amechi, gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako, gwamnan Jigawa, Sule Lamido, gwamnan Kwara, Abdulfatah Ahmed, da gwamnan Niger, Muazu Babangida Aliyu.

Saidai kuma zaune bata kare ba domin kuwa kakakin gwamnan Niger, Danladi Ndayebo, ya ce har yanzu gwamnan jihar Muazu Babangida Aliyu da takwaransa na jihar Jigawa Sule Lamido su na cikin jam'iyyar PDP daram.
Gwamnoni 'yan bakwai
.

Tuesday, November 26, 2013

Yadda bikin Kannywood ya kasance.

Ali Nuhu da Moblaze na coolfm
Ali Nuhu na kayatar da baki
Babs da Beebah na coolfm
Ishaq sidi Ishaq,da Iyan tama tare da mataimakin gwamna Abdullahi Umar Ganduje
Dr Abdullahi Umar Ganduje lokacin da yake jawabi
Gwamnan jihar Kaduna Alh Ramalan Yaro
Jerin manyan baki da suka halarci bikin
Sani Danja

A Ranar Asabar din da ta gabata ne aka gudanar da bikin bada kyaututtuka na Kannywood karo na farko da kamfanin sadarwa na MTN ya dauki nauyi. Bikin ya samu halartar mataimakin gwamna Dr Abdullahi umar Ganduje, gwamnan jihar Kaduna Alh Ramalan Yaro da Hakimin Dala Alh Aminu Ado da kuma masu ruwa da tsaki a harkar fina-finan kannywood. Daga cikin wadanda  bai wa kyaututtuka akwai Ali Nuhu, Nafisa Abdullahi, Sani Danja, Aminu Saira, Yakubu Muhammad, Zaharaddeen Sani ,Adam Zango dasauransu.Ga kuma hotuna na daga abin da ya samu a bikin domin kashe kwarkwatar idanunku.

Monday, November 25, 2013

A sha sauti lafia...



download
Sani Danger da Terry G -

                           http://www.hulkshare.com/9japride/sani-danja-ft-terry-g-basu-iyawa


                       Wakar sani danja da aka kaddamar ranar asabar din da ta gabata...ayi sauraro lafia.

Wednesday, November 20, 2013

Ziyarar Kwankwaso a kasar Jordan

Gwamna Kwankwaso tare da daliba Halima
Kwankwaso na tattaunawa da jami'an jami'ar kimiyya ta kasar Jordan
Gwamna Kwankwaso tare da mukarrabansa da kuma dalibai 'yan jihar Kano masu karatun digiri na biyu a kasar Jordan







Kunnenku nawa?!

Mawaki Terry G da Sani Danja
Ina masoyan mawakin nan kuma shahararren dan wasan Hausa Sani Danja? Gwanin na ku zai fito mu ku da sabuwar wakarsa wacce ya yi da mawakin kudun nan Terry G mai suna "Basu Iyawa" za a saki wannan waka a ranar 23 na watan nan da muke ciki..


Goron Gayyata...

A ranar Asabar 23 ga watan Nuwamba,ne za a gudanar da bikin  bada kyaututtuka na Kannywood karo na farko da kamfanin sadarwa na MTN zai dau nauyi tare da hadin gwiwar wasu kamfanoni goma sha daya. Za a gudanar da wannan bikin ne a dakin taro na "The Afficient" da karfe 8 na dare ...

Masu magana dai kan ce "Gani da ido maganin tambaya"...

Monday, November 18, 2013

Kwankwaso ya lashe kyautar zakaran gwamnoni ta bana.

Photo
Gwamna kwankwaso na karbar lambar yabo











Bikin Fina-finai na Afrika da aka gudanar a kasar Ingila ya karrama gwamnan jihar Kano Dr Rabi'u Musa Kwankwso saboda rawar da ya  ke takawa wajen inganta harkar ilimi da tallafawa  
   matasa. Yayin da  takwaransa na jihar Sakkwato Aliyu Wamako ya lashe kyautar zakaran gwamnoni a kan aiyukan raya kasa. 

Kwankwason ya bayyanawa manema labarai cewa wannan kyauta za ta kara masa karsashi wajen bunkasa ci gaban  matasa, gwamnan ya kuma yaba da hazaka ga daliban da suke karatu a can kasar ta Ingila.

Hausawa dai kan ce mai kamar zuwa kan aika!!!


Mahmud Abacha ya Angwance...



Hamama da Mahmud
 A  ranar Juma'ar da ta gabata ne aka daura auren dan tsohon shugaban kasa marigayi Sani Abacha, Mahmud Abacha da amaryarsa, 'yar gidan Alhaji Muhammad Ahman Abdulmulah,
Hamama Muhammad wanda aka gudanar a masallacin juma'a dake babban birnin tarayya Abuja.
Allah bada zaman lafia!!!
    
        

Sunday, November 17, 2013

Zaben Anambra ya bar baya da kura...






Malam Nasiru El-Rufa'i



Bayan tsare Malam Nasiru El-Rufai da aka yi a jiya har na tsawon awanni 23,yanzu dai ta tabbata cewa an sake shi,har ma ya yi martanin cewa gwamnan jihar Anambrar,Peter Obi ya tabbata cikakken sakarai, da ya bari aka yi amfani da shi wajen tauye hakkin 'yan kasa domin biyan muradin jam'iyar shugaban kasa.

 Hakan ta tabbata ne a cikin sakwanin tweeter da aka yi musaya tsakanin El-Rufa'in da wani mai suna Ubani Samuel, inda Ubanin ya yi ikrarin cewa su mutanen Anambra ba wawaye bane,shi kuma El-Rufa'in ya bashi amsa da cewa",sai dai gwanan ku Peter Obi soko ne"...

Baki ya san abin da zai fada amma bai san abinda za a fada masa ba!!!

Saturday, November 16, 2013

Abu kamar wasa...


Malam Nasiru el-Rufa'i
 Yanzu rahotanni suka shigo mana cewa 'yan sandan farin kaya wato SSS sun tsare  Malam Nasiru El-Rufa'i a wani otel dake Awka, wanda ya zo domin ya halarci zaben gwamna da ake yi a jihar ta Anambra.

 Ko mai ya yi zafi...idan ta yi tsami ma ji!!

Thursday, November 14, 2013

Abu namu...kura da kallabin kitse



https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEiOkPhMSrY8qqV2A8UZFUUFthOk7yl8kQOvChBYZDFFlTEnzrMYEY4WJoiQUxJjITIo9OzDqgt4iL5RYzdcXDt4K8sRdHWGTdVsL9L_aS_A_zwQxAxVCjZ9B1N6WampKrD7zI5RtBnWOhXc/s1600/1395968_10201365071023843_1689450719_n.jpg
Ahmad Adamu, sabon shugaban majalisar matasa kungiyar kasashe renon Ingila
Dan Nigeria, Ahmad Adamu ya dare  kan kujerar shugabancin majalisar matasa ta kungiyar kasashe renon Ingila,in da ya doke abokan takararsa daga kasashe ashirin,bayan zaben da aka yi a jiya,a ,a garin Hambantota na kasar Sri Lanka,a wajen taron kasashe renon Ingila karo na goma sha biyu.

Shi dai Ahmad Adamu, haifaffen jihar Katsina ne, wanda ya yi karatu a Jami'ar Bayero ta Kano, kuma ya ke da digirin-digir-gir a fannin tsimi- da-tanadi(Economics)a jami'ar Newcastle da ke kasar Ingila.

A shekarar 2011watan disamba ne, Ahmad ya kikiri kungiyar ci gaban matasa ta jihar Katsina,kuma shugabanta na farko,wacce kungiyar ke maida hankalinta akan magance rashin aikin yi da kuma tashe-tashen hankula, kuma sakatare ne a kwamitin gyaran tsarin mulki a shekara 2012 ,mai wakiltar Katsina ta tsakiya.

 Ita majalisar renon Ingila tana da mambobi miliyan dubu da dari biyu,sannan dan Nijeriya ne shugabanta, gaba-dai-gaba-dai Najeriya!!

To mu dai a nan sai mu ce Allah ya taya riko!!

Tuesday, November 12, 2013

Yadda taron bita ya kasance cikin hotuna.

Beebah ta coolfm a tsakiya
Sophie,da Dashen da Mary suna dansewa
kwalliyar amare daga sassan jihohi
Nadiya da Nabeela
Wacc ta shirya taro Lady Gwen
Jerin ire-iren kwalliyar amare
Daya daga cikin baki masu jawabi Hapsy Ibrahim
Jerin wasu mahalarta taron
Wasu daga cikin mahalarta taron
Mika godiya ga wadanda suka taka rawar gani a taron bitar
wasu baki

Monday, November 11, 2013

Kwarya ta bi kwarya...



Usman da Rukky
A ranar Asabar din da ta gabata ne ,Dan attajirin nan Marigayi Alhaji Usman Dantata ,kuma dan uwa ga attajirin nahiyar Afrika Alhaji Aliko Dangote,Usman Dantata(karami) ya auri 'yar hamshakin maikudin nan na jihar Borno Muhammad Indimi, Rukayya Indimi....
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEg4BYSlVocBR7lzjnAawPMj1tbfwaid383DONtXdfQTkZfQ0zmECDZjp23CLyP9vEObjSNWypRT7M5IRG3BKZt3uaVTjLEyiDiG9R5kD6BMnSRgeU01FS6wnRGDGvQGyFjoCfqzs_Rovahy/s1600/7.png
Usman da Rukky
Amarya Rukky kanwa ce ga matar Muhammad Babangida,Rahma. An daura auren ne a garin maiduguri yayin da aka koma babban birnin Tarayya domin shagalin biki...Abin ka da harkar manya mun ji ance wai an kashe akalla Naira miliyan 30 a bikin auren...
1.Amarya da Ango na Dancewa
2. kawayen amarya na takawa amarya da ango baya
       

Oh zamani riga...mai sa a manta da al'ada!!

Shugaba Jonathan ya Jika Samarin "Golden Eaglets" da miliyoyin kudi.

PHOTONEWS: FIFA U17 World Cup - Jonathan hosts victorious Golden Eaglets
Shugaba Jonathan tare da 'yan wasan golden Eaglets
 A jiya ne aka shiryawa 'yan wasan kasa da shekara 17 ,liyafar karramawa  da aka gudanar a fadar gwamnati dake Abuja bayan da suka lashe gasar kwallon kafa na matasa  'yan kasa da shekara17 ta duniya, da aka gudanar a hadaddiyar daular larabawa. Shugaba Jonathan ya yi wa 'yan wasa ruwan kudi inda aka bai wa:

 Kowanne dan wasa Naira miliyan biyu
 Mai horarwa  Naira miliyan uku
 Mataimakan mai horarwa miliyan biyu da rabi,kowanne
 Sauran masu tallafawa,wasu Naira dubu dari biyar,wasu kuma Naira dubu dari uku kowanne


PHOTONEWS: FIFA U17 World Cup - Jonathan hosts victorious Golden Eaglets
Daga hagu,Namadi sambo,kaptin kelechi Ihenacho, Manu Garba, Shugaba Jonathan ,Bamanga Tukur da Bolaji Abdullahi





Saturday, November 9, 2013

Najeriya ta lashe kopin matasa'yan kasa da shekara 17 karo na hudu.



Kungiyar matasa 'yan kasa da shekara 17 na murna bayan da suka karbi kopinsu
 A jiya ne kungiyar kwallon kafa ta matasa 'yan kasa da shekara 17 ta Najeriya ta lallasa takwararta ta kasar Mexico a wasan karshe da 3-0.
Wannan shi ya bai wa Najeriya dama na cin gasar kopin duniya ta matasa karo na hudu.

Har ila yau,a yau ne ministan wasanni Malam Bolaji Abdullahi zai tarbi kungiyar kwallon kafar, in da ake sa ran zasu dira a filin jirgin sama na Nnamdi azikwe dake babban birnin tarayya Abuja.

A gobe ne kuma, shugaba Goodluck Jonathan zai gana da 'yan wasan a wata gagarumar liyafa da aka shirya musu a fadar shugaban kasa in da ake sa ran masu ruwa da tsaki daga sassa na Najeriya za su halarci liyafar.

Friday, November 8, 2013

Abdulsamad Rabiu ya shiga sawun manyan attajiran Afrika.

Abdulsamad Rabiu
Mujallar "Forbes Afrika"ta wannan wata ta wallafa cewa Abdulsamad Rabiu ya shiga jerin manyan attajiran Afrika.

Abdulsamad haifaffan Kano ne,da ga mashahurin attajirin nan kuma malami sheik Isyaka Rabiu, wanda ya samu dukiyarsa ta hanyar kasuwanci bayan da Najeriya ta samu 'yanci kai daga turawan  mulkin mallaka, a shekarar 1970 mahaifin Abdulsamad ya shiga sawun attajiran lokacin kuma kusa a harkar siyasa.

Juyin mulkin da aka yi a 1983,da ya kuma kai ga capke shugaban kasa a lokacin Shehu Shagari, ya yi sanadiyar gurgunta arzikin Isyaka Rabiu, wanda a lokacin Abdulsamad na kasar Amurka inda yake karatun digirinsa.

Abdulsamad ya dawo gida Najeriya yana dan shekara 24,kuma ya tarar arzikin mahaifinsa ya durkushe, sai ya karbi ragamar kasuwancin mahaifin duk da bai goge a harkar ba.

Ya yi fadi-tashin da har ta kai ga ya zamo daga miloniya zuwa biloniya. Ci gaban da wannan gawurtaccen dan kasuwa ya samu na da nasaba da irin tsatsauran ra'ayoyin da ya bi na Ci gaba da harkokin kasuwancinsa gaba.

Abdulsamad dai ya fara kasuwanci a karan kansa bayan da ya samar da wani rukunin kafanin BUA wanda wannan kamfani yana daga cikin manyan kamfanoni a harkar sarrafa kayayyakin yau da kullum da kuma kasuwanci a Najeriya.

Rahotanni daga mujallarta "Forbes Africa" ta rawaito cewa rukunin kamfanin BUA ya yada hannuwa a bangarori da dama kamar yadda rukunin kamfanin Dangote ya yi.

Kamfanin BUA yana harkar gine-gine, da tama da karafa, da sarrafa kayayyaki,harkar manfetur da iskar gas,da harkar fito(sifirin jiragen ruwa),kuma kamfanin ya mallaki katafaren jirgin ruwa mai tsawon mita 200 na dakon siminti.

Abdulsamad ya kuma mallaki kadarori a kasar Ingila da kudinsa ya kai dala miliyan 62, da kuma kasar Afrika ta Kudu da kudinsa ya kai akalla dala miliyan 19 da gidan shakatawa da kudinsa ya kai dala miliyan 12 da dubu dari shida, yana kuma da jirgin sama kirar"jet",wanda kamfanin alfarman nan na "Rolls-Royce" ta kera injin,kuma kudin jirgin ya kai akalla dala miliyan 44 da dubu dari tara.

Hausawa dai kan ce sannu-sannu ba ta hana zuwa...sai dai a dade ba a baje ba...!!!

Wednesday, November 6, 2013

Da magani a gonar yaro...



Ganyen Zogale da 'ya'yansa
Zogale wani itace ne da Allah ya albarkace shi, kuma ya yawaita a fadin nahiyar Afrika. Har ila yau zogale ya fi wadatuwa lokacin Damina.
Zogale yana da sinadiran kara lafiya kamar su protein,Vitamin A da B, da kuma sinadarin Calcium, Iron da sauransu. Bincike ya nuna cewa Zogale yana maganin cututtuka akalla dari uku ko ma fiye da hakan, misali hawan jini, ciwon siga,sanyin kashi, gyanban ciki wato ulcer da ciwon da jan nama yake haddasawa da sauransu.
Amfaninsa....
  • Zogale yana da sinadiran da ya ke kara lafiya tsakanin yara da manya.
  • Yana maganin cututtuka da dama idan an yi  amfani da shi yadda ya kamata.
  • Yana karfafa garkuwa jiki domin yakar cututtuka.
  • Yana rage karsashin cutar kanjamau duk da dai bai zama yana iya warkar da ita gabadaya ba.
  • Yana watsakarwa.
Yadda ake sarrafa shi...
  • Ana kwadon  zogale,in da ake turarawa ko a dafa ganyen zogalen a hada shi da kuli-kuli, timatir, albasa, mankuli a cakude,wasu ma har sikari sukan sa.
  • Ana yajin sa,in da ake shanya ganyen zogalen a inuwa , idan ya bushe a hada da barkono a dake.
  • Ana shayin zogale, ruwan da aka dafa zogalen za a tace maimakon a zubar sai a sha.
  • Akan watsa ganyen zogalen  a miya a maimakon alaiyahu.
  • Haka kuma akan zuba karamin cokali(teaspoon) na dakakken zogale acikin tafasashen ruwa a hada  da zuma  da dan gishiri kadan,a gauraya a sha sau biyu a rana.
  • Akan dafa saiwar zogale da jar kanwa, a kuskure baki da shi domin maganin ciwon hakori.
  • Akan markada ganyen zogale kamar cikn hannu a hada da lemon Maltina dan rage yawan sitaci cikin jini.
  • Ana tauna 'ya'yan zogalen ko a hadiya  kamar kwayoyin magani.
  • Akan saka curin ganyen zogale a cikin ruwa domin tsaftace ruwan sha kamar yadda ake amfani da alumu.
"Wannan shi ne Nagge dadi goma"!!!

Monday, November 4, 2013

'Yan sanda sun yi yunkurin tarwatsa taron gwamnoni bakwai..


Daga hagu kawu Baraje, Sule Lamido,CSP Nnanna Amah , Rabiu Kwankwaso, da Musa Nyako
 Rahotanni sun bayyana cewa DPO na ofishin 'yansanda na Asokoro CSP Nnanna Amah ya yi wa gwamnoni bakwai dirar mikiya a yayin da suke tsaka da ganawa a gidan gwamnati dake Asokoro cikin babban birnin Tarayya Abuja.

CSP Nnanna ya shaida cewa yana bin umarni ne daga sama na ya dakatar da ganawar gwamnonin,inda su kuma suka bijere  suka ci gaba da taronsu.

Daga bisani dai taron ya tarwatse..



Babangida Aliyu, Kawu Baraje, Sule Lamido,CSP Nnanna, Rabiu Kwankwaso

Hausawa dai kan ce Karen bana shi ke maganin Zoman bana..!!

Ajali ya apkawa wata tawagar daurin aure a Borno....


'yan bindiga
Wasu 'yan bindiga sun kai wa ayarin motoci a Borno, da ake kyautata zaton 'yan daurin aure ne, hari, in da su ka kashe akalla  mutane sama da 30 ciki har da ango,a ranar Asabar din da ta gabata.

Rahotanni sun shaida  cewa an yiwa ayarin kantar bauna akan hanyar Bama zuwa Banki,a yayin da 'yan bikin suke kan hanyar su ta dawowa garin Maiduguri bayan shagalin biki da aka gudanar a Michikar jihar Adamawa.

Allah ya jikan wadanda suka rasu.

Masu iya magana dai kance idan ajali ya yi kira ko ba ciwo sai an je......

Saturday, November 2, 2013

Mai ka sani game da rayuwar Sani Danja?



An haifi shahararren dan wasan Hausan nan,  Sani Musa Danja a ranar 20 ga watan Afirilu shekara ta 1973, a karamar hukumar Fagge da ke cikin Jihar Kano. Ya kasance daya daga cikin 'ya'ya bakwai a wurin mahaifinsa Alhaji Musa Abdullahi da kuma mahaifiyarsa Hajia Risikat Musa.(wadanda dukkaninsu Allah ya dauki ran su).
 Sani Musa Danja

 Karatunsa...
Sani ya fara karatun firamarensa a makarantar Kano Capital daga shekara 1980-1985, inda ya tafi karamar sakandire ta kawaji a shekara 1985-1989, daga nan ya wuce babbar sakandire ta Rumfa  dake nan cikin Kano a shekara ta1989-1991, Sani bai tsaya anan ba ya cigaba da  karatu a kwalejin ilimi ta Tarayya FCE ta Kano, inda ya samu takardar shedar koyarwa ta NCE, harliyau ya koma FCE  domin karatun dipiloma a fanin koyan harkar mulki(Public Admin) a shekara ta 2004.

Fara waka...
Kasancewar Sani mai kwazo da kuma muryar iya waka,ya fara da raye-raye tun yana da shekara goma sha biyu kuma mawaki inda ya fara wake -wake da kungiyar" young kiddies voice",kasancewar sa muslimi kadai a wannan kungiya yasa ya balle.
Wakokinsa sun fara shahara ne  a fina-finan Hausa irinsu"yaki -taho-yaki" da sauransu, wanda a yanzu haka ya rera wakoki da dama cikin harshen hausa da turanci,Sani Danja bai tsaya anan ba har sai da ya kayatar da uwargidan shugaban kasa Patience Jonathan da wakokinsa a taron matan shugabannin kasa na Afrika.  Ya kuma yi wakoki a kasashe irinsu Niger, Ghana, Kamaru, Malaysia, ,Ingila da ma wasu kasashe goma. A yanzu haka wakokinsa(albam)  Mai farin jini  da "New guy in town" da  kuma ""Girl that i love"  na nan tafe.

Albam din mai farin jini
Harkar Fim..
Sani Danja ya fara harkar fim ne a shekarar 1999 da fim din sa mai suna Dalibai,sai kwarya ta bi kwarya    da Adon Kishiya duk  a shekara ta 2000, ya yi fina-finai akalla sama da dari shida wadanda ya shirya ya kuma ba da umarni daga cikin fittattu akwai Wasiyya wanda ya yi tare da Tahir Fagge da Kasimu Yaro,sai fim din Nagari wanda ya yi tare da Ali Nuhu sai fim irinsu Manakisa, Jaheed, Harsashi, Daham, Jarida, Jan kunne,Gambiza, Zuga-zugi,Tsumagiya da sauransu.Daga cikin masu tashe a yanzu akwai Daga Allah ne, Gani ga ka, Zo ki ji, Mai Nasara,Gudalliya, Burin Zuciya,  Nigeria da Niger, Basarake da sauransu. A yanzu haka Sani ya fadada harkar fim din sa da Nollywood inda ya yi fim da su Pete Edochie,Patience Ozorkor,Jim Iyke da sauransu .

A wajen shirya fim din  Idemili tare da Earnest Obi

Nasarori...
Sani Danja ya samu nasarar zama Jakada na daya daga cikin manyan kamfanin sadarwa na kasarnan ,haka kuma,ya yi aikin  hadin gwiwa da hukumar raya kasa ta Amurka wato USAID ta hanyar shirya fina-finai domin yaki da kanjamau da cutar shan inna,Ya kuma rike mukamin shugaban kunyiar 'yan fim na Hausa.Haka kuma jakada ne a kulub din Rotary,kuma jakadan zaman lafiya na majalisar dinkin duniya, kuma mamba ne na majalisar Matasa ta kasa, Shugan kasa Goodluck Jonathan ya kuma nada Sani Danja  a matsayin jakadan matasa bangaren wasanni.Baya ga haka,ya samu lambar yabo na "city people" a wannan shekara,haka kuma ya samu lambar yabo daga hukumar fasaha da al'adu ta kasa
Sani  da shugaba Jonathan
Sani Danja

Baya ga harkar fim da wakoki.......
Sani Danja ya kasance yana da shiri da yake gudanarwa na bada taimako ga marayu da,
masu karamin karfi,na daga abinci, kudi, da sauransu. 
A yanzu haka yana wani shiri a talabijin mai suna"Lokaci tare da Sani Danja"in da yake wayar da kan  jama'a akan masu dauke  da  cutar amosanin jini wato sikila, matsalolin da  suke fuskanta tare da hanyoyin dakile matsalar.
Sani na bada tallafi
A zamfara

Sani na bada tallafi ga masu cutar Polio
                                                       

Wasu daga cikin Fina-finan Sani da suke tafe...




Sani Musa Danja yana  da aure da 'ya'ya uku,Khadijatul Iman da Khalipha da Yakubu....