Tuesday, June 9, 2015

Bukola Saraki Ya zama Shugaban Majalisar Dattawa ta 8


Saraki SNP
Ayayin da ake rantsar da sanata Bukola Saraki
 An zabi Sanata Bukola Saraki a matsayin sabon shugaban Majalisar Dattawa ta Takwas.
Zaman Majalisar na Yau da Akawun Majalisar  Salisu Maikasuwa ya Jagoranta  ya samu halartar Sanatoci 57.
Saraki dake wakiltar Kwara ta tsakiya ya zamo shugaban majalisar dattawa bayan sanata Ahmad Yarima Da Deno Milaye suka gabatar da sunansa amatsayin dan Takara.

Yayin da a hannu guda,Ike Ekweremadu ya sake darewa akan mukaminsada ya rike a majalisa ta 7 amatsayin mataimakin shugaban majalisa.

Ekweremadu ya yi Nasarar kayar da abokin takararsa Sanata Ali Ndume.

Mai Martaba Sarkin Kano da Iyalansa

Mai Martaba  Sarkin Kano da Iyalansa


  A jiya 8 ga watan Yuni, Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya cika Shekara Daya akan Karagamar Mulki.