Monday, December 16, 2013

Ba a nakasashshe sai kasashshe...


Ibrahim yana kirga kudi da yatsun kafa.
















Ibrahim Amadu,dan shekaru 27 wanda dan asalin kauyen Kargo ne da ke cikin karamar Hukumar Sumaila ta jihar Kano da ke yawon bara a jihar Legas, ya shaida wa manema labarai cewa da yatsun kafarsa yake yin komai.inda yace ba abin da ba ya iya yi da yatsun kafarsa." Ina kirga kudi da su, ina ma’amala da wayar salula, don ina iya buga waya ina kuma iya amsawa. Ina yin gare-gare na yara da motar kara ta yaran kauye. Kuma da kaina nake gyaran janaretona idan ya samu matsala, ina sanya kaya. Ina yin abubuwa da yawa ba tare da an taimaka mini ba". 

Sai dai kuma ya bayyana cewa, ‘Akwai abubuwan da ba zan iya yi da kaina ba sai an taimaka mini, kamar wanka da wanke bahaya, wani lokaci ma sanya kaya yana yi mini wahala sai an taimaka mini. Ka san yadda rayuwa take ko wanda yake da hannaye biyu ma ba komai yake iya yi da kansa ba, wata rana sai ya nemi taimakon jama’a a wani abu. ya kuma gode wa Allah da Ya ba shi  damar yin wadansu abubuwa da yatsun kafarsa, yana fatan Allah Ya yi masa sakayya da gidan aljanna sakamakon wannan lalura da Allah Ya dora masa.’
Ya ci gaba da bayyanin cewa haka Allah ya halicce shi babu hannuwa biyu, amma  lafiyarsa kalau, don har matar aure yake da ita a garinsu.
Ya ce dole ce ta sanya yake barace-barace a kan titin Legas don ba shi da jarin da zai gudanar da harkar kasuwanci.
Ibrahim ya kara da cewa, zai daina yawon bara a Legas idan da zai samun tallafi daga ’yan siyasa da gwamnatoci.

 "Har wajen dan majalisarmu na je mai suna Kawu Sumaila don ya taimaka mini ya ba ni jari na bude shagon sayar da kaya amma sai ya ce na je garinmu na samu Sani Ahmed, da na je wurin Sani  ban samu komai ba, sai kawai na yanke shawarar na zo Legas na cigaba da bara don na samu jarin da zan fara sana’a a Kano".
Ibrahim ya kara da cewa" ko yanzu na samu tallafin jari da zan bude sana’ar saye da sayarwa zan bar bara na koma gida Kano"

Hausawa dai kan ce ba a maraya...sai rago

No comments:

Post a Comment