Jarumi Sani Muazu ( magana jari ce)da iyalinsa |
Thursday, January 30, 2014
Monday, January 27, 2014
Mai rabon ganin badi...
Allah sarki wannan bidiyo da kuke gani yaro ne aka ciro da ga burabuzai na gini sakamakon yaki da ake yi a kasar syria, a raye..Da ma masu iya magana kance mai rabon ganin badi...ko ana dakawa a turmi sai ya gani...
Friday, January 24, 2014
Jarumi Ali Nuhu ya musanta jita-jitan kara aure
Jarumi Ali Nuhu da iyalinsa |
Shahararren jarumin duniyar fina-finai na Kannywood da Nollywood Ali Nuhu ya musanta rade-radin da ake na cewa zai kara aure.
Jarumin ya musanta hakan ne a wata kafar yada labarai ta internet inda ya ce ba gaskiya bane, nema kawai ake a kunno masa wutar rikici a gidansa.
Dan haka ya yi kira ga jama'a da su yi watsi da rade-radin...
Thursday, January 23, 2014
Manoman shinkafa...kakarku ta yanke saka...
Shugan kasa Goodluck, Alh.Aliko da ministan kudi Ngozi Okonjo Iweala A garin Davos |
Ministan harkokin noma Akin Adesina wanda ya ke tare da attajirin a garin Davos dake kasar Switzerland domin halartar bikin bude taron tattalin arziki na duniya, ya shaida hakan ne a shafin sadarwar nan na twitter.
Wednesday, January 22, 2014
Liyafar Jikan marigayi Sani Abacha
A makon da ya gabata ne,jikan marigayi tsohon shugaban kasa Sani Abacha, Mubarak ya cika shekara uku a duniya ,mahaifiyarsa Gumsu ta shirya masa kwarya-kwaryar liyafa a makarantarsu dan taya shi murna.
Mahaifiyar Mubarak, Gumsu, 'ya ce ga marigayi Sani Abacha wacce ta auri wani attajirin kasar Kamaru Bayero Fadil a shekarar 1999 kuma Allah ya azurta auren da 'ya'ya biyar kuma Mubarak shi ne karamin cikin su.
Mu na taya Mubarak fatan alheri kuma Allah ya raya!!
Tuesday, January 21, 2014
Friday, January 17, 2014
Wednesday, January 15, 2014
Wai shin da gaske ne Baba Ari ya zama sarkin barkwanci?
Baba Ari |
Idan har da gaske ne..to mu na taya Baba Ari fatan alheri, Allah ya taya riko...
Monday, January 13, 2014
Tuna baya...
Yau wannan shafi zai yi duba ne akan wasu 'yan wasan Hausa na duniyar kannywod da suka kwanta dama.
Amina Garba(mama dumba)
Amina Garba |
A ranar 21 ga watan Nuwamba shekara ta 2010, duniyar Kannywood ta yi rashin uwa, Hajia Amina Garba wacce aka fi sani da mama dumba.
Jarumar ta rasu ne mawkwanni uku da ta sake aure sakamakon rashin lafia da ta dade tana fama da shi, , ta rasu tana da shekara 52.
Daga cikin fina-finan ta akwai Daham, Dan Almajiri, Jakada, Shelah, Tsintsiya, Jarida da sauransu
Marigayiyar ma'aikaciyar lafia ce ,wanda daga bisani ta fara drama a gidan talabijin na CTV kafin ta yi fice a harkar fim.
Hussaina Gombe |
Jarumar ta yi fice ne a fim din Hausa na barkwanci amatsayin maidakin Rabilu Musa(ibro).Ta rasu ne sanadiyar hatsarin mota da ya rutsa da ita da abokin aiki Shuaibu kulu akan hanyarsu ta dawowa daga Legos.
Maryam Aliyu |
Maryam Umar Aliyu
Jarumar ta rasu a ranar 12 ga watan Afrilu shekara 2010, sanadiyar rashin lafia wacce ta ke da nasaba da haihuwa.
Marigayiya ta tashi a Katsina ta kuma fara fim a shekara ta 2000 tauraruwarta kuma ta haska a shekara 2005. Daga cikin fina-finan ta akwai Khudisiyya, Jani, Labarin zuciya, Giwar mata, Makauniyar yarinya, Dan zaki, da saurauransu.
Ta auri jarumi Shuaibu Lawal(Kumurci), kuma kafin rasuwarta maidakin mawakin fina-finai Musbahu M. Ahmad ce.
Zilkiflu Muhammad
Zulkiflu Mohammed |
Dan wasa ne, darakta kuma Furodusa a duniyar Kannywood ta waccan lokaci, ya rasu a ranar 18 ga watan Fabrairu na shekarar 2010,Sanadiyar rashin lafia.
Daga cikin fim din sa akwai Aisha, Maqabuli, Ba'asi da sauran su.
Jamila Haruna
Jamila Haruna |
Ita ma fitacciyar 'yar wasa ce wacce ta ke yawan fitowa a matsayin uwa a cikin fina-finan Hausa, ta rasu a ranar 19 ga watan Afrilu shekara 2009, sanadiyar a hatsari a hanyar Suleja.
Daga cikin fim din ta akwai Furuci,Riba, Sangaya da sauransu.
Baraba Muhammad
Balaraba Muhammad |
Jaruma ce a duniyar kannywood na wancan lokaci, ta rasu 15 ga watan Maris shekara 2002 sanadiyar hatsarin mota kan hanyar kaduna zuwa kano,lokacin da ake shirin kawo ta dakin ta a matsayin amarya ga jarumi Shuaibu Lawan kumurci.
Daga cikin fina-finan ta akwai Furuci, Dawayya , Buri da sauransu.
Ahmed S.Nuhu |
Shahararren jarumin ya rasu ne ranar 1 ga watan Jinairu 2007,sakamakon hatsarin mota a kan hanyar Azare.
Daga cikin fina-finan sa akwai Linzami da wuta, Huznee, Mujadala,Akasi da sauransu.
Kafin rasuwarsa furodusa ne a kampanin shirya fina-finai na FKD, kuma maigida ga jaruma Hafsat Shehu.
Hauwa Ali Dodo |
Ta na daga cikin jaruman 'yan wasa da suka gina duniyar ta Kannywood, ta rasu 1 ga watan Jinairu 2010 sakamakon hadarin mota a garin Sami-naka.
Daga cikin fina-finanta akwai Ki yarda da ni, Sangaya, Daski da ridi, Buri, Na gari da sauransu.
Wasu daga cikin 'yan Kannywood da suka rigamu gidan gaskiya, sune;
Maijidda Mustapha-16 Yuni 2001
Safiya Ahmad-26 Fabrairu 2010
Darakta Lawal Kaura-13 Disamba 2011
Darakta Muhammad Balarabe Sango-1 Disamba 2012
Darakta Aminu Hassan Yakasai-16 Yuni 2001
Aisha Kaduna(Shamsiya)
Shuaibu Danwanzan
Nura MUhammed
Umar Katakore da sauran su.
Aisha Kaduna(Shamsiya)
Shuaibu Danwanzan
Nura MUhammed
Umar Katakore da sauran su.
Allah ya jikan su ya gafarta musu.
Friday, January 10, 2014
Tuesday, January 7, 2014
Monday, January 6, 2014
Mahdi mai dogon Zamani...
Ali Nuhu |
Jarumin wanda tauraronsa ya ke ci gaba da haskawa ya fara fim ne a shekara 1999 da fim din Abin sirri ne,wanda kama yanzu ya yi fice a Kannywood da takwararta na Nollywood. Ya kuma samu karramawa tun daga cikin gida har Kasashen ketare.
Hira da Aminu Momoh
Aminu A.Shariff(momoh) |
Ya yi karatun Diploma a jami'ar Bayero a fannin ilimin kare aukuwar laifuffuka wato"Crime Management, prevention and Control",Sannan ya koma ya yi digirinsa na farko a fannin Siyasa wato "Political Science". Ya yi aure a shekarar 2001 kuma yana da 'ya'ya hudu, Muhammad ,Safiyya, Aisha da Aliyu.
Abin da ya ja hankalinsa ya shiga fim
Sha'awa da ra'ayi su ne suka sa momoh ya shiga harkar fim, kuma domin ya samu abin dogaro da kai, da taimakawa rayuwar al'umma.
Ya fara da fim din "ayi dai mu gani" daga nan ya cigaba da harkar fina-finai.Daga cikin fina-finan sa akwai Sanafahana, Sirrin boye, Abu naka,Hadizalo, Kishiya ko 'Yar uwa, Ni Matar aure ce, Tuwon tulu, Duniyar sama, Najeriya da Nijar da sauransu
Nasarori
Jarumin ya bayyana babbar nasarar sa shi ne haduwa da jama'a, taimakawa ta bangaren addini ,da kuma canza rayuwar wasu ta bangarori da dama, tare kuma da tabbatar da zaman lafia tsakanin al'ummu da kabilu, duk ta sanadiyar fim .
Baya ga harkar fim..
Momoh ya shaida mana cewa yana kasuwanci wanda shi ne sana'ar gidansu,yana aiyukan sa kai, da kuma harkokin siyasa.
Aminu Momoh, Nadiya, Fati Bararoji |
Tallafin Dangote ga jiharsa ta Haihuwa
Alhaji Aliko Dangote |
Haka kuma gidauniyarsa ta Dangote Foundation ta bada tallafin dala miliyan goma shabiyu ga asibitin Murtala .
Sabon Salo...barawo da sallama...
Tsinken cin abinci mai fanka |
To jama'a sai a nemi tsiken domin kwasar malmalar tuwo!!
Mawaki Naziru Ahmad ya kara aure...
Ango Nazir da Amarya Khadija |
Mu na taya ango da amarya fatan alheri,kuma Allah ya baiwa ango ikon yin adalci...
Friday, January 3, 2014
Shin kuskure ne hadewar bangarorin Najeriya da turawa suka yi?
Saidai har yanzu bayan shekaru dari wasu na ganin kwalliya bata biya kudin sabulu ba, hasali ma kuskure ne hade sassan ba tare da la'akari da bambamce-bambamcen da ke tsakanin al'umomin yankunan ba.
Idan aka yi la'akari da muhinman zarge-zargen tsohon shugaban kasa Cif Olushegun Obasanjo ya yi a kwanannan a wasikar da ya rubutawa shugaban kasa Jonathan, za a ga ashe baya ba zani aka yi , dan kuwa bambamcin kabila da addini sun yi matukar tasiri a harkar gudanar da mulkin kasarnan, abin da wadansu su ke wa kallon sababin rugujewar kasar, idan har ba a samu hazikin shugaban da zai kawo daidaito a tsakanin mabambamtan al'umomin kasarnan ba.
Allah sarki mutuwa rigar kowa.
Marigayiya Hauwa Ali Dodo(Biba problem) |
Idan ba a manta ba Hauwa Ali(Biba problem)fitaciyar jaruma ce da ta bada gudummawa wajen gina duniyar Kannywood ,wasu daga cikin manyan fina-finanta akwai Ki yarda dani, Sangaya, Daskin da ridi, Buri, Na gari, Gaskiya dokin karfe, da sauransu.
Allah ya jikanta ya gafarta mata...
Thursday, January 2, 2014
Wednesday, January 1, 2014
Kwan-ci-tashi...yau shekara bakwai da rasuwar Ahmed S.Nuhu
Marigayi Ahmed S. Nuhu |
Allah sarki, a rana mai kama ta yau, daya ga watan jinairu shekara dubu biyu da bakwai ne, shahararren dan fim din Hausa nan na duniyar Kannywood Ahmed S. Nuhu ya kwanta dama sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi akan hanyar Azare.
Allah ya jikanshi,ya gafarta masa, mu kuma ya kyautata namu zuwan.
Wasu 'Yan wasa da suka bace...sun dawo!
| ||
Ibrahim Mandawari |
Aminu Sharif Ahlan |
Ku na da masaniyar cewa wasu shahararrun 'yan wasa na duniyar kannywood sun fara bayyana bayan da suka yi batan dabo?
Wadanan 'yan fim ba wasu bane illa Ibrahim Mandawari, da Abba Al-Mustapha da Aminu Sharif Ahlan...
Rahotanni sun ishe mu cewa Al-Mustapha da Sharif har sun bayyana a wani sabon fim wanda ake ikirarin ya fita daban da sauran fina-finai saboda dukiyar da aka kasha a fim din.
Subscribe to:
Posts (Atom)