Wednesday, January 1, 2014

Dangote ya hau shafin twitter



Shafin Dangote na twitter
Rahotanni sun bayyana cewa fitaccen attajirin nan Alhaji Aliko Dangote ya bi sawun masu amfani da shafin sadarwar nan na twitter, sai ku lalube shi ta @AlikoDangote. Duk da dai bai fara dora sakwanni akan shafin ba, amma tuni mabiya shafin nasa suka kai akalla dubu daya da dari biyu da ashirin da biyar.

No comments:

Post a Comment