Thursday, January 23, 2014

Manoman shinkafa...kakarku ta yanke saka...





Shugan kasa Goodluck, Alh.Aliko da ministan kudi Ngozi Okonjo Iweala A garin Davos
Hamshakin attajirin nan  na Afrika kuma dan jihar Kano Alhaji Aliko Dangote ya sake   daura aniyar sanya hannun jari na zunzurutun kudin da ya kai dala miliyan dari uku a harkar noman shinkafa a kasarmu Najeriya.

Ministan harkokin noma Akin Adesina wanda ya ke tare da attajirin a garin Davos dake kasar Switzerland domin halartar bikin bude taron tattalin arziki na duniya, ya shaida hakan ne a shafin  sadarwar nan na twitter.

No comments:

Post a Comment