Monday, January 6, 2014

Mawaki Naziru Ahmad ya kara aure...


Photo: TASKAR FIM: Nazir M. Ahmad Ya Angonce

An daura auren shahararren mawakin nan, Nazir M. Ahmad, da aka fi sani da Sarkin Waka, a yau, a masallacin Murtala Muhammad, dake cikin birnin Kano.

Mawakin da suka sha doguwar soyayya da fitacciyar jarumar finafinan nan, Hadiza Gabon, jim kadan bayan daura auren na sa, ya bayyana wa wakilin #RARIYA cewa ba zai iya misalta farin cikinsa a wannan rana ba, sannan yana godiya ga duk wadanda suka halarci daurin auren, tare da yi musu addu'ar koma wa gidajensu lafiya. A karshe kuma ya nemi masoyansa su taya shi addu'ar Allah ya albarkanci auren na su.
Ango Nazir da Amarya Khadija
A jiya ne shahararen mawakin nan Naziru Ahmad ya angwance da sahibarsa Khadija. An daura auren ne a masallacin murtala da ke cikin Kano, daga bisani aka gwangwaje a liyafar da aka gudanar a Otal din Royal Tropicana, dake cikin Kano .

Mu na taya ango da amarya fatan alheri,kuma Allah ya baiwa ango ikon yin adalci...

No comments:

Post a Comment