Friday, January 3, 2014

Allah sarki mutuwa rigar kowa.


Marigayiya Hauwa Ali Dodo(Biba problem)
 A ranar daya ga watan jinairun shekara dubu biyu da goma ne ,yau shekara hudu kenan da fitacciyar jarumar Hausa fim Hauwa Ali Dodo da aka fi sani da Biba problem ta kwanta dama sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da ita a garin saminaka dake jihar kaduna.

Idan ba a manta ba Hauwa Ali(Biba problem)fitaciyar jaruma ce da ta bada gudummawa wajen gina duniyar Kannywood ,wasu daga cikin manyan fina-finanta akwai Ki yarda dani, Sangaya, Daskin da ridi, Buri, Na gari, Gaskiya dokin karfe, da sauransu.

Allah ya jikanta ya gafarta mata... 

No comments:

Post a Comment