Yau wannan shafi zai yi duba ne akan wasu 'yan wasan Hausa na duniyar kannywod da suka kwanta dama.
Amina Garba(mama dumba)
Amina Garba |
A ranar 21 ga watan Nuwamba shekara ta 2010, duniyar Kannywood ta yi rashin uwa, Hajia Amina Garba wacce aka fi sani da mama dumba.
Jarumar ta rasu ne mawkwanni uku da ta sake aure sakamakon rashin lafia da ta dade tana fama da shi, , ta rasu tana da shekara 52.
Daga cikin fina-finan ta akwai Daham, Dan Almajiri, Jakada, Shelah, Tsintsiya, Jarida da sauransu
Marigayiyar ma'aikaciyar lafia ce ,wanda daga bisani ta fara drama a gidan talabijin na CTV kafin ta yi fice a harkar fim.
Hussaina Gombe |
Jarumar ta yi fice ne a fim din Hausa na barkwanci amatsayin maidakin Rabilu Musa(ibro).Ta rasu ne sanadiyar hatsarin mota da ya rutsa da ita da abokin aiki Shuaibu kulu akan hanyarsu ta dawowa daga Legos.
Maryam Aliyu |
Maryam Umar Aliyu
Jarumar ta rasu a ranar 12 ga watan Afrilu shekara 2010, sanadiyar rashin lafia wacce ta ke da nasaba da haihuwa.
Marigayiya ta tashi a Katsina ta kuma fara fim a shekara ta 2000 tauraruwarta kuma ta haska a shekara 2005. Daga cikin fina-finan ta akwai Khudisiyya, Jani, Labarin zuciya, Giwar mata, Makauniyar yarinya, Dan zaki, da saurauransu.
Ta auri jarumi Shuaibu Lawal(Kumurci), kuma kafin rasuwarta maidakin mawakin fina-finai Musbahu M. Ahmad ce.
Zilkiflu Muhammad
Zulkiflu Mohammed |
Dan wasa ne, darakta kuma Furodusa a duniyar Kannywood ta waccan lokaci, ya rasu a ranar 18 ga watan Fabrairu na shekarar 2010,Sanadiyar rashin lafia.
Daga cikin fim din sa akwai Aisha, Maqabuli, Ba'asi da sauran su.
Jamila Haruna
Jamila Haruna |
Ita ma fitacciyar 'yar wasa ce wacce ta ke yawan fitowa a matsayin uwa a cikin fina-finan Hausa, ta rasu a ranar 19 ga watan Afrilu shekara 2009, sanadiyar a hatsari a hanyar Suleja.
Daga cikin fim din ta akwai Furuci,Riba, Sangaya da sauransu.
Baraba Muhammad
Balaraba Muhammad |
Jaruma ce a duniyar kannywood na wancan lokaci, ta rasu 15 ga watan Maris shekara 2002 sanadiyar hatsarin mota kan hanyar kaduna zuwa kano,lokacin da ake shirin kawo ta dakin ta a matsayin amarya ga jarumi Shuaibu Lawan kumurci.
Daga cikin fina-finan ta akwai Furuci, Dawayya , Buri da sauransu.
Ahmed S.Nuhu |
Shahararren jarumin ya rasu ne ranar 1 ga watan Jinairu 2007,sakamakon hatsarin mota a kan hanyar Azare.
Daga cikin fina-finan sa akwai Linzami da wuta, Huznee, Mujadala,Akasi da sauransu.
Kafin rasuwarsa furodusa ne a kampanin shirya fina-finai na FKD, kuma maigida ga jaruma Hafsat Shehu.
Hauwa Ali Dodo |
Ta na daga cikin jaruman 'yan wasa da suka gina duniyar ta Kannywood, ta rasu 1 ga watan Jinairu 2010 sakamakon hadarin mota a garin Sami-naka.
Daga cikin fina-finanta akwai Ki yarda da ni, Sangaya, Daski da ridi, Buri, Na gari da sauransu.
Wasu daga cikin 'yan Kannywood da suka rigamu gidan gaskiya, sune;
Maijidda Mustapha-16 Yuni 2001
Safiya Ahmad-26 Fabrairu 2010
Darakta Lawal Kaura-13 Disamba 2011
Darakta Muhammad Balarabe Sango-1 Disamba 2012
Darakta Aminu Hassan Yakasai-16 Yuni 2001
Aisha Kaduna(Shamsiya)
Shuaibu Danwanzan
Nura MUhammed
Umar Katakore da sauran su.
Aisha Kaduna(Shamsiya)
Shuaibu Danwanzan
Nura MUhammed
Umar Katakore da sauran su.
Allah ya jikan su ya gafarta musu.
No comments:
Post a Comment