Friday, January 3, 2014

Shin kuskure ne hadewar bangarorin Najeriya da turawa suka yi?



Wannan hoto da ku ke gani an dauke shi ne a ranar 1 ga watan Jinairu 1914, lokacin da gwamna janar na wancan lokaci Lord Lugard ya hade yankunan Arewaci da Kudancin kasar nan ta zama dunkulalliyar kasa, sa'annan  maidakinsa Flora Shaw ta rada mata suna Najeriya a bisa la'akari da kogin kuwara(da turawa ke wa lakanin Niger) da ya karade kasar.

Saidai har yanzu bayan shekaru dari wasu na ganin kwalliya bata biya kudin sabulu ba, hasali ma kuskure ne hade sassan ba tare da la'akari da bambamce-bambamcen da ke tsakanin al'umomin yankunan ba.

Idan aka yi la'akari da muhinman zarge-zargen tsohon shugaban kasa Cif Olushegun Obasanjo ya yi a kwanannan a wasikar da ya rubutawa shugaban kasa Jonathan, za a ga ashe baya ba zani aka yi , dan kuwa bambamcin kabila da addini sun yi matukar tasiri a harkar gudanar da mulkin kasarnan, abin da wadansu su ke wa kallon sababin rugujewar kasar, idan har ba a samu hazikin shugaban da zai kawo daidaito a tsakanin mabambamtan al'umomin kasarnan ba.

No comments:

Post a Comment