Monday, January 6, 2014

Hira da Aminu Momoh





Aminu Shariff Aminu Shariff(momoh)
Aminu A.Shariff(momoh)
An haifi  shahararren dan wasan fim  din Hausa Aminu Aliyu Shariff  da aka fi sani da Momoh a ranar 7 ga watan fabrairu 1977 a gwalen jihar Kano, ya yi karatu a Gwale fimare,daga nan  ya tafi kwalejin malamai ta Gumel ya kuma karasa a Kwalejin Rumfa dake Kano.

 Ya yi karatun Diploma a jami'ar Bayero a fannin ilimin kare aukuwar laifuffuka wato"Crime Management, prevention and Control",Sannan ya koma ya yi digirinsa na farko a fannin Siyasa wato "Political Science". Ya yi aure a shekarar 2001 kuma yana da 'ya'ya hudu, Muhammad ,Safiyya, Aisha da Aliyu.


Abin da ya ja hankalinsa ya shiga fim
Sha'awa da ra'ayi su ne suka sa momoh ya shiga harkar fim, kuma domin ya samu abin dogaro da kai, da taimakawa rayuwar al'umma.
 Ya fara da fim din "ayi dai mu gani" daga nan  ya cigaba da harkar fina-finai.Daga cikin fina-finan sa  akwai Sanafahana, Sirrin boye, Abu naka,Hadizalo, Kishiya ko 'Yar uwa, Ni Matar aure ce, Tuwon tulu, Duniyar sama, Najeriya da Nijar da sauransu

Nasarori
Jarumin ya bayyana babbar nasarar sa shi ne haduwa da jama'a, taimakawa ta bangaren addini ,da kuma canza rayuwar wasu ta bangarori da dama, tare kuma da tabbatar da zaman lafia tsakanin al'ummu da kabilu, duk ta sanadiyar fim .

Baya ga harkar fim..
Momoh ya shaida mana cewa yana kasuwanci wanda shi ne sana'ar gidansu,yana aiyukan sa kai, da kuma harkokin siyasa.


Aminu Momoh, Nadiya, Fati Bararoji

No comments:

Post a Comment