Mai martaba SAN Kano Alhaji Ado Bayero |
Da sanyin safiyar yau Juma'a 6 ga watan Yunin shekara 2014 ne rahotanni suka ishe mu cewa Allah ya yi wa Mai Martaba sarkin Kano Alhaji Ado Bayero rasuwa bayan ya sha fama da rashin lafia. Za a yi Jana'izarsa bayan da misalin karfe hudu na yamma,in da ake saran za a binne shi a makabartar Masarautar dake gidan sarki na unguwar Nassarawa
An Haifi Mai martaba Alhaji Ado Bayero a ranar 25 ga watan Yulin shekarar 1930,ya hau karagar mulki a shekara ta 1963 yana da shekara 33 a duniya , kuma ya kasance Sarkin Kano na 13 karkashin tutar fulani. Mai martaba Alhaji Ado ya kasance da ga sarkin Kano Abdullahi Bayero kuma jikan Sarkin Kano Muhammad Abbas.
Dr.Ado Bayero ya riki mukamin jakadan kasar Sinigal,inda daga nan ne ya dare karagar mulki.
Ashekarar da ta gabata ne wasu masu tada kayar baya suka kai wa tawagar Sarkin ayayin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga bikin saukar Alqur'ani acikin birnin Kano.Kafin bikin cikarsa shekaru 50 akan karagar mulki.
Mai martaba Sarkin Kano ya rasu yana da shekaru 84 a duniya. Ya bar 'ya'ya 62, maza 30 mata 32.
Allah ya jikan sa ya gafarta masa,Yasa Aljanna makoma...
No comments:
Post a Comment