Sarkin Kano Muhammadu Sanusi 11 |
A yau ne mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na 11 ya ziyarci wadanda harin Bam ya rutsa dasu a makarantar koyon aikin duba gari wato School of Hygiene a jiya.
Sarkin ya yi tir da wannan hari tare da kira da a gaggauta dora wadanda suka samu karaya sakamakon harin. Ya kuma yi ta'aziya ga wadanda suka rasa rayukansu tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.
Rahotanni sun bayyana cewa Wamban Kano Abbas Sanusi da Jarman Kano farfesa Isa Hashim na daga cikin tawagar da suka yiwa sarkin rakiya.
Haka kuma kwamishinan Lafiya ta jiha Dr Abubakar Labaran Yusuf da ta sa tawagar sune suka tari sarkin.
Idan ba a mantaba a jiya ne bam ya fashe a makarantar aikin duba gari wato school of Hygiene,a yayin da dalibai suke tsaka da yin rajistar kakar karatu,inda mutane 9 suka rasa rayukansu sama da mutane 20 suka jikkata.
Maimartaba yana dubiya |
Allah ya tsare ya kuma kiyaye gaba...
No comments:
Post a Comment