Saturday, November 2, 2013

Mai ka sani game da rayuwar Sani Danja?



An haifi shahararren dan wasan Hausan nan,  Sani Musa Danja a ranar 20 ga watan Afirilu shekara ta 1973, a karamar hukumar Fagge da ke cikin Jihar Kano. Ya kasance daya daga cikin 'ya'ya bakwai a wurin mahaifinsa Alhaji Musa Abdullahi da kuma mahaifiyarsa Hajia Risikat Musa.(wadanda dukkaninsu Allah ya dauki ran su).
 Sani Musa Danja

 Karatunsa...
Sani ya fara karatun firamarensa a makarantar Kano Capital daga shekara 1980-1985, inda ya tafi karamar sakandire ta kawaji a shekara 1985-1989, daga nan ya wuce babbar sakandire ta Rumfa  dake nan cikin Kano a shekara ta1989-1991, Sani bai tsaya anan ba ya cigaba da  karatu a kwalejin ilimi ta Tarayya FCE ta Kano, inda ya samu takardar shedar koyarwa ta NCE, harliyau ya koma FCE  domin karatun dipiloma a fanin koyan harkar mulki(Public Admin) a shekara ta 2004.

Fara waka...
Kasancewar Sani mai kwazo da kuma muryar iya waka,ya fara da raye-raye tun yana da shekara goma sha biyu kuma mawaki inda ya fara wake -wake da kungiyar" young kiddies voice",kasancewar sa muslimi kadai a wannan kungiya yasa ya balle.
Wakokinsa sun fara shahara ne  a fina-finan Hausa irinsu"yaki -taho-yaki" da sauransu, wanda a yanzu haka ya rera wakoki da dama cikin harshen hausa da turanci,Sani Danja bai tsaya anan ba har sai da ya kayatar da uwargidan shugaban kasa Patience Jonathan da wakokinsa a taron matan shugabannin kasa na Afrika.  Ya kuma yi wakoki a kasashe irinsu Niger, Ghana, Kamaru, Malaysia, ,Ingila da ma wasu kasashe goma. A yanzu haka wakokinsa(albam)  Mai farin jini  da "New guy in town" da  kuma ""Girl that i love"  na nan tafe.

Albam din mai farin jini
Harkar Fim..
Sani Danja ya fara harkar fim ne a shekarar 1999 da fim din sa mai suna Dalibai,sai kwarya ta bi kwarya    da Adon Kishiya duk  a shekara ta 2000, ya yi fina-finai akalla sama da dari shida wadanda ya shirya ya kuma ba da umarni daga cikin fittattu akwai Wasiyya wanda ya yi tare da Tahir Fagge da Kasimu Yaro,sai fim din Nagari wanda ya yi tare da Ali Nuhu sai fim irinsu Manakisa, Jaheed, Harsashi, Daham, Jarida, Jan kunne,Gambiza, Zuga-zugi,Tsumagiya da sauransu.Daga cikin masu tashe a yanzu akwai Daga Allah ne, Gani ga ka, Zo ki ji, Mai Nasara,Gudalliya, Burin Zuciya,  Nigeria da Niger, Basarake da sauransu. A yanzu haka Sani ya fadada harkar fim din sa da Nollywood inda ya yi fim da su Pete Edochie,Patience Ozorkor,Jim Iyke da sauransu .

A wajen shirya fim din  Idemili tare da Earnest Obi

Nasarori...
Sani Danja ya samu nasarar zama Jakada na daya daga cikin manyan kamfanin sadarwa na kasarnan ,haka kuma,ya yi aikin  hadin gwiwa da hukumar raya kasa ta Amurka wato USAID ta hanyar shirya fina-finai domin yaki da kanjamau da cutar shan inna,Ya kuma rike mukamin shugaban kunyiar 'yan fim na Hausa.Haka kuma jakada ne a kulub din Rotary,kuma jakadan zaman lafiya na majalisar dinkin duniya, kuma mamba ne na majalisar Matasa ta kasa, Shugan kasa Goodluck Jonathan ya kuma nada Sani Danja  a matsayin jakadan matasa bangaren wasanni.Baya ga haka,ya samu lambar yabo na "city people" a wannan shekara,haka kuma ya samu lambar yabo daga hukumar fasaha da al'adu ta kasa
Sani  da shugaba Jonathan
Sani Danja

Baya ga harkar fim da wakoki.......
Sani Danja ya kasance yana da shiri da yake gudanarwa na bada taimako ga marayu da,
masu karamin karfi,na daga abinci, kudi, da sauransu. 
A yanzu haka yana wani shiri a talabijin mai suna"Lokaci tare da Sani Danja"in da yake wayar da kan  jama'a akan masu dauke  da  cutar amosanin jini wato sikila, matsalolin da  suke fuskanta tare da hanyoyin dakile matsalar.
Sani na bada tallafi
A zamfara

Sani na bada tallafi ga masu cutar Polio
                                                       

Wasu daga cikin Fina-finan Sani da suke tafe...




Sani Musa Danja yana  da aure da 'ya'ya uku,Khadijatul Iman da Khalipha da Yakubu....









No comments:

Post a Comment