Wednesday, November 6, 2013

Da magani a gonar yaro...



Ganyen Zogale da 'ya'yansa
Zogale wani itace ne da Allah ya albarkace shi, kuma ya yawaita a fadin nahiyar Afrika. Har ila yau zogale ya fi wadatuwa lokacin Damina.
Zogale yana da sinadiran kara lafiya kamar su protein,Vitamin A da B, da kuma sinadarin Calcium, Iron da sauransu. Bincike ya nuna cewa Zogale yana maganin cututtuka akalla dari uku ko ma fiye da hakan, misali hawan jini, ciwon siga,sanyin kashi, gyanban ciki wato ulcer da ciwon da jan nama yake haddasawa da sauransu.
Amfaninsa....
  • Zogale yana da sinadiran da ya ke kara lafiya tsakanin yara da manya.
  • Yana maganin cututtuka da dama idan an yi  amfani da shi yadda ya kamata.
  • Yana karfafa garkuwa jiki domin yakar cututtuka.
  • Yana rage karsashin cutar kanjamau duk da dai bai zama yana iya warkar da ita gabadaya ba.
  • Yana watsakarwa.
Yadda ake sarrafa shi...
  • Ana kwadon  zogale,in da ake turarawa ko a dafa ganyen zogalen a hada shi da kuli-kuli, timatir, albasa, mankuli a cakude,wasu ma har sikari sukan sa.
  • Ana yajin sa,in da ake shanya ganyen zogalen a inuwa , idan ya bushe a hada da barkono a dake.
  • Ana shayin zogale, ruwan da aka dafa zogalen za a tace maimakon a zubar sai a sha.
  • Akan watsa ganyen zogalen  a miya a maimakon alaiyahu.
  • Haka kuma akan zuba karamin cokali(teaspoon) na dakakken zogale acikin tafasashen ruwa a hada  da zuma  da dan gishiri kadan,a gauraya a sha sau biyu a rana.
  • Akan dafa saiwar zogale da jar kanwa, a kuskure baki da shi domin maganin ciwon hakori.
  • Akan markada ganyen zogale kamar cikn hannu a hada da lemon Maltina dan rage yawan sitaci cikin jini.
  • Ana tauna 'ya'yan zogalen ko a hadiya  kamar kwayoyin magani.
  • Akan saka curin ganyen zogale a cikin ruwa domin tsaftace ruwan sha kamar yadda ake amfani da alumu.
"Wannan shi ne Nagge dadi goma"!!!

1 comment: