Friday, November 8, 2013

Abdulsamad Rabiu ya shiga sawun manyan attajiran Afrika.

Abdulsamad Rabiu
Mujallar "Forbes Afrika"ta wannan wata ta wallafa cewa Abdulsamad Rabiu ya shiga jerin manyan attajiran Afrika.

Abdulsamad haifaffan Kano ne,da ga mashahurin attajirin nan kuma malami sheik Isyaka Rabiu, wanda ya samu dukiyarsa ta hanyar kasuwanci bayan da Najeriya ta samu 'yanci kai daga turawan  mulkin mallaka, a shekarar 1970 mahaifin Abdulsamad ya shiga sawun attajiran lokacin kuma kusa a harkar siyasa.

Juyin mulkin da aka yi a 1983,da ya kuma kai ga capke shugaban kasa a lokacin Shehu Shagari, ya yi sanadiyar gurgunta arzikin Isyaka Rabiu, wanda a lokacin Abdulsamad na kasar Amurka inda yake karatun digirinsa.

Abdulsamad ya dawo gida Najeriya yana dan shekara 24,kuma ya tarar arzikin mahaifinsa ya durkushe, sai ya karbi ragamar kasuwancin mahaifin duk da bai goge a harkar ba.

Ya yi fadi-tashin da har ta kai ga ya zamo daga miloniya zuwa biloniya. Ci gaban da wannan gawurtaccen dan kasuwa ya samu na da nasaba da irin tsatsauran ra'ayoyin da ya bi na Ci gaba da harkokin kasuwancinsa gaba.

Abdulsamad dai ya fara kasuwanci a karan kansa bayan da ya samar da wani rukunin kafanin BUA wanda wannan kamfani yana daga cikin manyan kamfanoni a harkar sarrafa kayayyakin yau da kullum da kuma kasuwanci a Najeriya.

Rahotanni daga mujallarta "Forbes Africa" ta rawaito cewa rukunin kamfanin BUA ya yada hannuwa a bangarori da dama kamar yadda rukunin kamfanin Dangote ya yi.

Kamfanin BUA yana harkar gine-gine, da tama da karafa, da sarrafa kayayyaki,harkar manfetur da iskar gas,da harkar fito(sifirin jiragen ruwa),kuma kamfanin ya mallaki katafaren jirgin ruwa mai tsawon mita 200 na dakon siminti.

Abdulsamad ya kuma mallaki kadarori a kasar Ingila da kudinsa ya kai dala miliyan 62, da kuma kasar Afrika ta Kudu da kudinsa ya kai akalla dala miliyan 19 da gidan shakatawa da kudinsa ya kai dala miliyan 12 da dubu dari shida, yana kuma da jirgin sama kirar"jet",wanda kamfanin alfarman nan na "Rolls-Royce" ta kera injin,kuma kudin jirgin ya kai akalla dala miliyan 44 da dubu dari tara.

Hausawa dai kan ce sannu-sannu ba ta hana zuwa...sai dai a dade ba a baje ba...!!!

No comments:

Post a Comment