|
Sabon Wazirin Kano Sa'ad Shehu Gidado |
A ranar Juma'a 20 ga watan Yunin shekarar da muke ciki Sarkin Kano Mhammadu Sanusi 11 ya nada sabon Wazirin Kano.
Waziri Gidado shi ne wand ya maye gurbin sheik Nasir Muhammad Nasir da aka tube bayan marigayi Sarkin Kano Ado Bayero sakamakon rashin amincewar gwamnatin Kano.
Maimartaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu, ya yi kira ga sabon wazirin Kano Sa'adu Shehu Gidado daya baiwa masarautar Kano shawarwarin da suka dace akan al'amuran da suka shafi addini dama walwalar jama'a.
Sarkin wanda ya shaida hakan,yayin bikin nadin sabon wazirin ,ya bayyana cewa daga cikin muhimman aiyukan shi sune bada shawarwari a harkokin addinin musulunci da kuma hanyoyin warware matsaloli.
Haka kuma sarki ya yi kira ga sabon waziri da yayi koyi da halayen kwarai na tsohon waziri inda ya yi amfani da mukaminsa wajen dabbaka musulunci da ma jihar Kano.
An haifi Gidado a shekarar 1966 a unguwar Kurawa dake nan Kano.Yayi makarantar Firamare ta Jar kasa daga shekarar 1972 zuwa 1978,daga nan ya tafi makarantar Sakandire ta koyon Arabiya dake Gwale daga shekarar 1980 zuwa 1986. Haka kuma ya yi karatu a makarantar koyon harkar sdhari'a wato Legal daga shekarar 1986 zuwa 1989.
Har ila yau kafin nadinsa Gidado Magatakarda ne a majalisar Masarautar Kano tun a shekara 2001.
Sabon Waziri da ne ga marigayi waziri Shehu Gidado wa ga marigayi Isa Waziri.
Allah ya taya riko...