Wasu 'yan majalisar Najeriya na son a cire takwarorinsu da basa goyon bayan Baraje
A Najeriya, yayin da 'yan majalisun dokokin tarayya
suka koma bakin aiki ranar Talata, shugaban 'sabuwar PDP', Abubakar Kawu
Baraje, ya kai wa 'yan majalisar ziyara.
Wasu 'yan majalisar dai sun bijirewa yunkurin hana Alhaji Baraje shiga majalisar, sai dai wasu sun goyi bayan shigarsa, suna masu cewa kotun kasar ma ta amince da kasancewarsa shugaban wani bangare na jam'iyar ta PDP.
Wasu 'yan majalisar dai sun shaidawa manema labarai cewa suna so su cire wasu daga cikin jagororin majalisar wadanda suke gani ba sa tare da bangaren Alhaji Baraje.
Barajen wanda ya samu rakiyar bijirarrun gwanonin nan guda bakwai da suka hada da gwamna Rotimi Ameachi na jihar Ribas da Rabiu Kwankwaso na jihar Kano da Sule Lamido na jihar Jigawa da Babangida Aliyu na jihar Niger da Aliyu Magatakarda Wamako na jihar Sokoto da kuma Abdul fatah na jihar Kwara sai Murtala Nyako na jihar Adamawa. Sai dai, ziyarar tasa ta samu nakasu a yayinda wasu 'yan majalisa masu biyayya ga jagorancin Bamanga Tukur suka tada yamutsi akokarinsu na hana a saurari jawabin Alh. Barajen.
Wannan hairani ya jawo yaga rigar dan majalisa Dakuku Peterside mai wakiltar jihar Ribas da wani dan majalisa mai wakiltar jihar Bayelsa ya yi. Wannan ce ta raba kan 'yan majalisar gida biyu tsakanin magoya bayan Bamanga da na Kawu Baraje abinda ya sabbaba kakakin majalisar Aminu Tambuwal jan kunnen 'yan siyasa da su kaucewa yin kalamai da ka iya yamutsa hazo a dandalin siyasar Najeriya.
Hausawa dai kan ce"a juri zuwa rafi,watarana a fashe tulu"!!!!!!!!
No comments:
Post a Comment