Gwamnatin tarayya ta amince da kashe karin dala miliyan dari kowacce shekara domin yaki da kwayar cutar kanjamau da take nema ta zama annoba a kasar.
Ministan lafiya na Najeriya Onyebuchi Chukwu ya bayyana haka a wajen wani taro kan yaki da cutar kanjamau da aka gudanar a jihar Lagos. Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin tarayya zata ci gaba da bada karfi wajen yaki da cutar kanjamau. Yace shugaban Najeria Goodluck Jonathan ya bayyana shirin da yake da shi na yaki da cutar kanjamau tare da kara yawan kudin da ake kashewa kowacce shekara da dala miliyan dari.
Ministan ya bayyana cewa, gwamnatin tana kokari sosai a yaki da zazzabin cizon sauro, yace an raba sama da gidan sauro miliyan sittin tsakanin shekara ta dubu biyu da goma zuwa yanzu. Banda haka kuma yace ana kyautata zaton cewa, a watan Disamba zata a tabbatar da cewa yanzu Najeriya ta shawo kan kurkunu. Dr. Chuku yace yanzu an yi shekara hudu ba a sami wani dauke da cutar kurkunu ba
No comments:
Post a Comment