An daura auren ne a babban masallacin Abuja,wanda babban limamin
masallacin, Ustaz Musa Muhammed ya jagoranta.
Daurin auren ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Arc.Namadi
Sambo, tsofaffin shuwagabannin kasa janar Ibrahim Babangida da janar
Abdulsalami abubakar, sai ministan babban birnin tarayya Abuja Alh. Bala
Mohammed.
Yayin da kasaitacciyar liyafa ta biyo baya a dakin taro na Thisday Dome
dake garin na Abuja. Anan ma liyafar ta samu halatar gwamnan jihar Gombe Alh
Ibrahim Dankwambo, da na jihar Taraba Alh Garba Umar, sai sanatoci irinsu Andy
Uba da Paulinius Igwe,daga hamshakan masu kudi kuwa akwai Alh Aliko Dangote da
Femi Otedola da sauransu. Kai har ma
da Hamza Al mustapha!!
Soyayya ruwan zuma |
Ango da amarya |
Manyan baki |
Shagali |
Hotunan Kafin biki |
ALLAH YA BA DA ZAMAN LAFIYA,
YA KAWO KAZANTAR DAKI!!!!!!!!!!!!
No comments:
Post a Comment