Kaikayin ido na nufin duk wani bakon abu da ya taba ido, kamar kasa, kura, burbushin katako, fenti, ko karfe.
Idan ido na ruwa, ko kaikayi, ko ya yi ja, ko radadi ko alamun makalewar wani abu a cikin ido, ko kuma gani garara-garara, duk alamu ne na kaikayin ido da kwalliyar ido, ko gajia, ko yaduwar cuta ke haddasawa.
Yadda za a magance sun hada da :
- A rinka amfani da tibarau a duk sa'ilin da ake iska, domin kare ido daga kura ko tsakuwa.
- Mata su rinka yin kwalliya sai-sa-sai-sa, ka da a wuce gona-da iri.
- Ka da a rinka fesa turare ko magungunan kwari dab da fuska, idan za a yi, a fesa inda yake da wadatuwar iska.
- A guji sosa ido, musamman idan aka yi mu'amalla da sinadaran da ka iya sanya kaikayin ido.
- A garzaya asibiti idan kaikayin ido ya tsananta.
No comments:
Post a Comment