Wata 'yar Najeriya mai suna Aisha Ajibola Obabiyi mai shekaru ashirin da daya daliba a jami'ar jihar Ikko ta lashe gasar da aka kira - mace musulma ta gari -- wadda aka shirya musamman domin mata musulmi na duniya.
Mata 20 ne suka shiga gasar daga Indonesia, da Iran, da Nigeria, da Brunei da kuma Bangladesh. Alkalan gasar sun yi la'akari ne da imanin matan da basirarsu da kuma iya karatun al-Kura'ani .
Daga cikin kyaututtukan da aka ba ta har da kujerar Makkah, da kudi kwatankwancin kudin Najeriya sama da miliyan uku da kuma yawon bude idanu zuwa kasar Indiya.
Hausawa dai sun ce "hali shi ne mace, ba launin fata ba"
No comments:
Post a Comment