Akalla mata dubu takwas ne,su ka yi tattaki zuwa hukumar Hisbah ta jihar zamfara domin neman agajin gwamnatin jihar ta nema musu mazajen aure.
Matan, wadanda shugabar kungiyar zawarawa ta jihar Hajia Suwaiba Isa da Uban kungiyarAlh.Sa'idu Goshi suka jagoranta, Sun bayyana rashin jin dadin yadda suke zaune kara zube babu abin yi.
Alh.Sa'idu ya bayyana cewa kungiyar na da mata akalla sama da dubu takwas wadanda suka hada da zawarawa dubu biyar da dari uku da tamanin, wadanda mazan su suka mutu akalla dubu biyu da dari biyu sai marayu dubu daya da dari biyu da sauransu,wanda ya shaida cewa su na neman mazan aure wadanda za su dauki dawainiyarsu.
Idan ba a manta ba hukumar Hisba ta jihar kano ita ta fara gudanar da wannan shiri,inda aka aurar da dubban zawarawa kashi-kashi da taimakon gwamnatin jihar Kano.
Masu iya magana kan ce abin da ya koro bera ya fada wuta ya fi wutar zafi....!!!
No comments:
Post a Comment