Monday, September 30, 2013

Gwamnatin Kano ta kudiri aniyar kawar da miyagun dabi'u.











Gwamnan jihar Kano Dr. Rabi'u  Musa Kwankwaso

 Gwamnatin jihar Kano ta lashi takobin yaki da rashin da'a a tsakanin al'ummarta.

Kwamishiniyar ma'aikatar al'amuran mata Dr. Binta Tijjani Jibril ta shaidawa manema labarai hakan, in da ta ce gwamnatin Kano ta kudiri aniyar magance tallace-tallace, da barace-barace da shaye-shaye tsakanin matasa da kuma aikatau.

Dr.Binta, ta kara da cewa gwamnatin Kano baza ta lamunci masu yi mata zagon kasa ba, a kokarin da take na inganta rayuwar al'ummar jiharta.

Acewarta, ma'aikatar ta himmatu ne wajen tabbatar da da'a tsakanin al'umma ganin yadda munanan dabi'u ke kokarin wofintar da kokarin gwamnati na inganta rayuwar al'umma.

Hausawa dai kan ce..gyara kayanka ba ya zama sauke mu raba!!!

Cool fm ta cika shekara biyu a yayin da Najeriya ta cika shekaru hamsin da uku.



 




Gidan rediyon cool fm Kano zai bijiro da wani kasaitaccen shiri dan murnar cikarsa shekara biyu da kafuwa a Kano, tare da murnar cikar Najeriya hamsin da uku da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka.

Za a gudanar da wannan biki ne a wani salo na ba-sa-bam-ba, inda mashahuran masu gabatar da shirye-shirye za su kasance masu rabon abinci a wajen wata liyafa da gidan rediyon zai gabatar. A wani wurin cin abinci na"Save Mart" da ke kan titin Ahmadu Bello cikin birnin Kano, a gobe Talata 1 ga watan Oktoba shekara 2013 da karfe shida na yamma akan kudi Naira dubu uku kacal.

Maza nemi na ka tikitin shiga wannan kasaitacciyar liyafa a harabar gidan rediyon da ke gidan gona wato Farmcentre.

Friday, September 27, 2013

Zawarawa a Zamfara sun bi sawun takwarorinsu na Kano.

                                                          

Akalla mata dubu takwas ne,su ka yi tattaki zuwa hukumar Hisbah ta jihar zamfara domin neman agajin gwamnatin jihar  ta nema musu mazajen aure.

Matan, wadanda shugabar kungiyar zawarawa ta jihar Hajia Suwaiba Isa da Uban kungiyarAlh.Sa'idu Goshi suka jagoranta, Sun bayyana rashin jin dadin yadda suke zaune kara zube babu abin yi.

Alh.Sa'idu ya bayyana cewa kungiyar na da mata akalla sama da dubu takwas wadanda suka hada da zawarawa dubu biyar da dari uku da tamanin, wadanda mazan su suka mutu akalla dubu biyu da dari biyu sai marayu dubu daya da dari biyu da sauransu,wanda ya shaida cewa su na neman  mazan aure wadanda za su  dauki dawainiyarsu.

Idan ba a manta ba hukumar Hisba ta jihar kano ita ta fara gudanar da wannan shiri,inda aka aurar da  dubban zawarawa kashi-kashi da taimakon gwamnatin jihar Kano.

Masu iya magana kan ce abin da ya koro bera ya fada wuta ya fi wutar zafi....!!!

Allah ya yi.........Zaharadeen ya angwance!!


Zahradeen da Amina

Zahradeen da Amina

Nan da sa'oi ne shahararren dan wasan Hausa Zaharaddeen Sani zai angwance da tsaleliyar amaryarsa Amina Hussain wanda za a yi  a yau dinnan a massallacin Aminudeen cikin birnin Kano da misalin karfe biyu na rana  Juma'a 27 ga watan satumba shekara 2013.


Allah ya bada zaman lafia,ya kuma bada zuri'a tayyaba.......!!

Wednesday, September 25, 2013

Ku ceci 'ya'yanku daga sharrin na'urar intanet.....



Na'urar intanet na daga cikin kere-keren da suka fi shahara a wannan karni, wanda kuma ta shiga ran al'umma. Kusan yanzu babu al'ummar da ba ta amfani da na'urar intanet.

Saidai wannan na'ura na da bangarori biyu na alherinta da rashinsa
Ta bangaren alherinta akwai: bincike,karance-karance domin fahimtar addini, harkar ciniki na zamani da sauransu. Ta bangaren sharrinta akwai: kallon batsa da ka iya bata tarbiya da zamba cikin aminci da sauransu.

Wani abin takaicin shi ne yadda dimbin jama'a ciki har da musulmai su ka fi karkata ga sharrin na'urar ta intanet kuma galibin masu kallon hotunan batsan matasa ne.
A wani bincike game da shafin nan na matambayi baya bata wato google, an bayyana cewa musulmai na daga cikin jerin masu mu'amalla da wadannan shafuka na batsa.

Wadannan shafuka su na gurbata tarbiyar matasan mu ta hanyar karkatar da su daga tafarkin addini.
Dan haka yana da kyau, iyayen da 'ya'yansu suke ta'amalli da wannan na'ura su sa idanu wajen tabbatar da 'ya'yansu na amfani da shi ta hanyar da ya kamata.

Haka kuma ,yana da kyau a ajiye kwamfiyuta a sarari yadda yara ba za su kebance wurin amfani da ita su kadai ba.

Haka kuma akwai dabarun toshe irin wadannan munanan shafuka yadda matasan ba za su kai gare su ba.
Har ila yau,ya kamata gwamnatocin kasashen musulmi su dau tsauraran matakai na toshe irin wadannan kafofi...

Gyara kayan ka....ba ya taba zama sauke mu raba.....!!!


























Hanyoyin magance kaikayin ido.....




Kaikayin ido na nufin duk wani bakon abu da ya taba ido, kamar kasa, kura, burbushin katako, fenti, ko karfe.

Idan ido na ruwa, ko kaikayi, ko ya yi ja, ko radadi ko alamun makalewar wani abu a cikin ido, ko kuma gani garara-garara, duk alamu ne na kaikayin ido da kwalliyar ido, ko gajia, ko yaduwar cuta ke haddasawa.


Yadda za a magance sun hada da :
  • A rinka amfani da tibarau a duk sa'ilin da ake iska, domin kare ido daga kura ko tsakuwa.
  • Mata su rinka yin kwalliya sai-sa-sai-sa, ka da a wuce gona-da iri.
  • Ka da a rinka fesa turare ko magungunan kwari dab da fuska, idan za a yi, a fesa inda yake da wadatuwar iska.
  • A guji sosa ido, musamman idan aka yi mu'amalla da sinadaran da ka iya sanya kaikayin ido.
  • A garzaya asibiti idan kaikayin ido ya tsananta.
Lafiya uwar jiki....babu mai fushi dake!!!!

Friday, September 20, 2013

Sabuwar jam'iyar PDP ta zargi fadar shugaban kasa da makarkashiyar sauya shugabanci a majalisar dokokin Najeriya.

majalisar dokoki
majalisar wakilai

           



majalisar dattijai
  


Sabuwar jam'iyar PDP ta zargi fadar shugaban kasar Najeriya da yin makarkashiyar tsige shugaban majalisar dattijai David Mark da takwaransa kakakin majalisar wakilai Aminu Tambuwal.

Sai dai fadar gwamnatin ta musanta zargin inda ta danganta zargin amatsayin yarfe ne na 'yan adawa.

Zargin ya biyo bayan wani yunkurin kafa kingiya da tsagin masu yiwa Bamanga Tukur biyayya suka kafa domin sanyawa kakakin ido da niyyar zakulo aibinsa.

A nasa bangaren sakataren sabuwar jam'iyyar PDP Chukwuemeka Eze ya gargadi masu shirin kulla wannan makirci su sake tunani.
Hausawa dai kan ce "Idan za ka gina ramin mugunta gina shi gajere".....

Thursday, September 19, 2013

Dangote kai kadai gayya....



 
  Alh.Aliko Dangote


Kama ta ya yi batun yadda rukunin kamfanonin Dangote ya kammala shirye-shirye domin kafa harsashin gina matatar mai mafi girma a nahiyar Afrika, ta sanya 'yan Najeriya tsalle da dokin cewa a karshe kasarsu ta kubuta daga kwamacalar da ta tsince kanta aciki ta kuma kama tafarkin kai wa ga matsiyinta na giwar Africa.

Matsalar karacin man fetir, matsala ce da ta dade ta na ciwa shuwagabanin siyasar Nijeriya tuwo a kwarya da kuma har yanzu suke kasa warware ta, duk da kasancewar kasa a sahun gaba wajen samar da
danyen man fetir.

Wanna shafin, zai bayyana muku yadda wannan sanarwa ta zama wani abin alfahari a tsakanin 'yan Nijeriya tun bayan da kasar ta gano manfetur, domin kuwa kafa katafariya matatar mai zai kasance wani al'amari da ya dara samun man alheri.
Anan muna iya cewa Dangote zai jefi tsuntsu biyu da dutse daya.

Matsalar wutar lantarki, ita ce kan gaba wajen dakile kokarin 'yan Nijeriya na samun cigaba, kasancewar gwannati ta gaza a wannan fanni. To kaga anan, idan manfetir ya wadatu, 'yan Nijeriya zasu sarrafa shi wajen samar da wutar lantarkin. Wanda hakan kadai ma ya isa ya 'yanta dimbin basirar sana'oi da Allah ya albarkaci matasan Nijeriya da shi.

Kuma hakan zai rage yawan gurbatar iska da hayakin da dan karamin janaetan nan da 'yan Najeriya ke yiwa lakani da "I pass my neighbour" (na dara makwabci na).
Hakan zai kawo mashahurin sauyi ta yadda 'yan Nijeriya da suka yi gudun hijira zuwa makwabtan kasashe domin yin sana'oi zasu dawo gida.
.
Alfanun da kafa wannan matatar mai zai samar sun hada da : Dakile matsalar almundahana, idan aka tuna  da yadda aka yi amfani da batun tallafin manfetir wajen wawure kudaden 'yan Najeriya da rana tsaka. To ka ga anan, idan matatar nan ta fara aiki,zata rufe kafar bukatar siyo tataccen mai daga kasashenketare,ka ga batun tallafin shigo da tataccen mai ya kau.

Kamfanin Dangote ya sha samun nasarori, duba ga  cewa kamfanin simintin sa,na daya daga cikin aiyukanda aka fara,aka kuma kammala akan lokaci. Kuma a iya  kudin da aka iyakance wajen kammala su.
Akwai abin ban mamaki yadda shuwagabannin Najeriya suka kasa warware matsalolin kasar duk da cewa yawankudin da suke da shi ya dama na Dangote, ammairin nasarorin da ya samu babu wani dan siyasar da zai bugi kirji ya ja da shi.

Galibin mutane sun zaci da injinan janareta ake samar da lantarkin da ake gudanar da manyan masana'antu a kasashen da suka cigaba,kasancewar a Najeriya. Injin janareta shi ne babbar hanyar samar da wutar lantarki ga kowa, har ma da masu hannu da shunin da suka mallaki jiragen kawunansu.
Shin wannan bai zama tamkar tupka da warwara ba?

Abin mamaki ana shi ne gazawar wadannan shugabannin siyasa ya gaza tadiye irin nasarorin da Dangoten ya samu, yadda gwamnatoci suka gaza wajen samar da wutar lantarki amma shi ya samar da ita da rukunin kamfanoninsa ya samu.

A ra'ayi na,abin da 'yan Najeriya ke bukata shi ne a samu karin irin su Dangote, ba wai 'yan siyasa ba. Dan haka duk sa'ilin da 'yan Najeriya suka yi addu'a kamata ya yi su roki karin masu zuciya irin su Dangote ba wai mayaudaran 'yan siyasa ba.

Akalla dai ace an samu wanda ya samar da wutar lantarki,duk da cewa dai ta takaita ga rukunin kamfanoninsa.
Hausawa dai na cewa "girma ya fadi da Rakumi ya shanye ruwan 'yan tsaki"

'Yar Najeriya ta lashe gasar mace mafi kyaun hali

Aisha Ajibola da kofin gasar
Aisha Ajibola
Aisha Ajibola a lokacin da cinye gasar

Wata 'yar Najeriya mai suna Aisha Ajibola Obabiyi  mai shekaru ashirin da daya daliba a jami'ar jihar Ikko ta lashe gasar da aka kira - mace musulma ta gari -- wadda aka shirya musamman domin mata musulmi na duniya.

An gudanar da gasar ce a birnin Jakartar kasar Indonesia a matsayin kishiya ga gasar zaben sarauniyar kyau ta duniya.

Mata 20 ne suka shiga gasar daga Indonesia, da Iran, da Nigeria, da Brunei da kuma Bangladesh. Alkalan gasar sun yi la'akari ne da imanin matan da basirarsu da kuma iya karatun al-Kura'ani .


Daga cikin kyaututtukan da aka ba ta har da kujerar Makkah, da kudi kwatankwancin kudin Najeriya sama da miliyan uku da kuma yawon bude idanu zuwa kasar Indiya.

Hausawa dai sun ce "hali shi ne mace, ba launin fata ba"

Wednesday, September 18, 2013

Ziyarar Baraje ta jawo baiwa hammata iska a majalisar wakilan Najeriya..




 

 Wasu 'yan majalisar Najeriya na son a cire takwarorinsu da basa goyon bayan Baraje



A Najeriya, yayin da 'yan majalisun dokokin tarayya suka koma bakin aiki ranar Talata, shugaban 'sabuwar PDP', Abubakar Kawu Baraje, ya kai wa 'yan majalisar ziyara.

Ziyarar dai tana da dangantaka da rabuwar da jam'iyyar PDP ta yi inda wasu gwamnoni da jiga-jiganta, ciki har da 'yan majalisun dokokin suka balle.
Wasu 'yan majalisar dai sun bijirewa yunkurin hana Alhaji Baraje shiga majalisar, sai dai wasu sun goyi bayan shigarsa, suna masu cewa kotun kasar ma ta amince da kasancewarsa shugaban wani bangare na jam'iyar ta PDP.
Wasu 'yan majalisar dai sun shaidawa  manema labarai cewa suna so su cire wasu daga cikin jagororin majalisar wadanda suke gani ba sa tare da bangaren Alhaji Baraje.

Barajen wanda ya samu rakiyar bijirarrun gwanonin nan guda bakwai da suka hada da gwamna Rotimi Ameachi na jihar Ribas da Rabiu Kwankwaso na jihar Kano da Sule Lamido na jihar Jigawa da  Babangida Aliyu na jihar Niger da Aliyu Magatakarda Wamako na jihar Sokoto da kuma Abdul fatah na jihar Kwara sai Murtala Nyako na jihar Adamawa. Sai dai, ziyarar tasa ta samu nakasu a yayinda wasu 'yan majalisa masu biyayya ga jagorancin Bamanga Tukur suka tada yamutsi akokarinsu na hana a saurari jawabin Alh. Barajen.
Wannan hairani ya jawo yaga rigar dan majalisa Dakuku Peterside mai wakiltar jihar Ribas da wani dan majalisa mai wakiltar jihar Bayelsa  ya yi. Wannan ce ta raba kan 'yan  majalisar gida biyu tsakanin magoya bayan Bamanga da na Kawu Baraje abinda ya sabbaba kakakin majalisar Aminu Tambuwal jan kunnen 'yan siyasa da su kaucewa yin kalamai da ka iya yamutsa hazo a dandalin siyasar Najeriya.

Hausawa dai kan ce"a juri zuwa rafi,watarana a fashe tulu"!!!!!!!!

Tuesday, September 17, 2013

Speta janar na 'yansandan Najeriya ya angwance..

Speta janar na 'yan sandan  Najeriya Mohammed Abubakar, ya angwance da Zarha 'yar tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja, Alh Ibrahim Bunu a ranar asabar din da ta gabata.
An daura auren ne a babban masallacin Abuja,wanda babban limamin masallacin, Ustaz Musa Muhammed ya jagoranta.
Daurin auren ya samu halartar mataimakin shugaban  kasa Arc.Namadi Sambo, tsofaffin shuwagabannin kasa janar Ibrahim Babangida da janar Abdulsalami abubakar, sai ministan babban birnin tarayya Abuja Alh. Bala Mohammed.
Yayin da kasaitacciyar liyafa ta biyo baya a dakin taro na Thisday Dome dake garin na Abuja. Anan ma liyafar ta samu halatar gwamnan jihar Gombe Alh Ibrahim Dankwambo, da na jihar Taraba Alh Garba Umar, sai sanatoci irinsu Andy Uba da Paulinius Igwe,daga hamshakan masu kudi kuwa akwai Alh Aliko Dangote da Femi Otedola da sauransu. Kai har  ma da Hamza Al mustapha!!
Soyayya ruwan zuma

Ango da amarya











Manyan baki
Shagali
Hotunan Kafin biki













ALLAH YA BA DA ZAMAN LAFIYA, YA KAWO KAZANTAR DAKI!!!!!!!!!!!!

Gwamnatin Najeriya Zata Rika Kashe Naira Miliyan 100 kan Yaki Da cutar kanjamau Kowacce Shekara


Gwamnatin tarayya ta amince da kashe karin dala miliyan dari kowacce shekara domin yaki da kwayar cutar kanjamau da take nema ta zama annoba a kasar.
Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan
Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan
Gwamnatin ta bayyana cewa, za a gudanar da shirin ne domin inganta hanyoyoyin yaki da cutar a cikin gida a maimakon ci gaba da dogara ga kasashen waje, wanda hakan kuma zai zama taimako a kokarin yaki da cutar kafin shekara ta dubu biyu da goma sha biyar.