Wednesday, February 24, 2016

Allah ya yi wa 'yar Kannywood Aisha Dankano Rasuwa

 Image result for images of Aisha Dankano
A ranar Talata ne 23 ga watan Fabrairu Allah ya yi wa Shahararriyar 'yar  Fim din Kannywood rasuwa da rana.
Marigayiyar ta rasu bayan 'yar gajeriyar jinya..Kuma tuni aka yi jana'izarta a Unguwar Gwammaja acikin birnin Kano.

Kafin rasuwar ta kasance fitacciya a harkar fina-finan Hausa na Kannywood ,Kadan daga cikin fina-finanta sun hada da Zawarawa,Uwar mugu,Teburin mai shayi,Mai dalilin aure, Zeenat, Jamhuriya Kishiya ko 'yar Uwa, Kayar Ruwa da sauran makamantansu...Ta  rasu tana da shekaru 34 a duniya.
Allah ya jikanta ya gafarta mata

No comments:

Post a Comment