Wednesday, October 2, 2013

Martanin Kwankwaso a kan taron kasa..









Dr. Rabiu Musa Kwankwaso
Gwamnan jihar Kano Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana kiraye-kirayen a gudanar da taron kasa ya sabawa tsarin damokradiya kuma tagwaita aiyukan zababbun 'yan majalisa ne.


Gwamnan ya bayyana hakan ne, a wata ganawa da manema labarai da ya yi a Kano, a yayin bikin cikar Najeriya hamsin da uku da samun 'yancin kai. Ya kuma shaida cewa  taron ba komai zai haifar ba illa fama rauni, maimakon kamo bakin zaren matsalolin da ke addabar kasa, in da ya jaddada cewa al'umar Najeriya babu abin da su ke bukata illa tabbatacciyar wutarlantarki, da kayayyakin more rayuwa.

Gwamna Kwankwaso, ya kuma kara da cewa bayan shekaru hamsin da uku da samun 'yancin kai, har yanzu 'yan Najeriya na fama da yunwa tare da yanke kauna saboda matsalar cin hanci da rashin kyakkyawan shugabanci.

Dakta Kwankwaso, ya kuma shaida cewa matsalar karancin kudi da ke addabar kasa bai shafi jihar Kano ba saboda tsantsaini da hangen nesan shugabanninta.

Ya kuma dora laifin rashin gudanar da zabubbukan kananan hukumomi a jihar Kano, a kan matsalar tsaro, da soke rajistar wasu jam'iyu da aka yi a baya, da kuma sabarta-juyartar siyasa da addabar Najeriya.

Allah dai ya kiyashe mu da taron shan shayi...!!!

No comments:

Post a Comment