Cuta aka ce ba mutuwa ba ..domin kuwa mai dakin gwamnan jihar Bauchi Hajiya Hadiza Muhammad Abubakar ta kawo dauki ga mara lafiyarnan mai fama da da cutar snkarar mama, Sa'adatu Muhamad Giade.
Hotan wannan matashiya ,mai shekaru 19 a duniya kuma marainiya ya karade kafar intanet wadda take a kwance a Asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa magashiyyan sakamakom cutar sankarar mama.
Acewar sanarwar da jami'in yada labaran mataimakin gwamnan jihar Bauchi Yakubu Adamu ya fitar, Uwargidan gwamnan ta kawo daukin ne ta hannun kungiyarta B-SWEEP dake bada tallafi inda ta bukaci a mika bayanan maralafiyar tare da sanar da mahukuntan asibitin cewa ta dau dawainiyar Sa'adatu Muhammad Giade dan haka a kula da lafiyarta.
Sa'adatu Allah ya kara lafiya.
No comments:
Post a Comment