A ranar Talata ne 23 ga watan Fabrairu Allah ya yi wa Shahararriyar 'yar Fim din Kannywood rasuwa da rana.
Marigayiyar ta rasu bayan 'yar gajeriyar jinya..Kuma tuni aka yi jana'izarta a Unguwar Gwammaja acikin birnin Kano.
Kafin rasuwar ta kasance fitacciya a harkar fina-finan Hausa na Kannywood ,Kadan daga cikin fina-finanta sun hada da Zawarawa,Uwar mugu,Teburin mai shayi,Mai dalilin aure, Zeenat, Jamhuriya Kishiya ko 'yar Uwa, Kayar Ruwa da sauran makamantansu...Ta rasu tana da shekaru 34 a duniya.
Allah ya jikanta ya gafarta mata
No comments:
Post a Comment