A yau ne Sarkin Saudiya Salman Al Saud ya budewa shugaban kasa da ayarinsa cikin dakin Ka'aba amatsayin wata girmamawa ga shugaban.
Sarkin wanda shi ne yake kula da manyan masallatan Makka da Madina, ya bada umarni a budewa shugaba Buhari dakin Ka'aba
Daga cikin wadanda suka shiga dakin mda shugaban kasa sun hada da mai martaba sakin Kano Muhammad Sanusi na biyu da gwamnonin jihohin Zamfara Abdul Aziz Yari da Khashim Shettima na Borno da na jihar Katsina Aminu Masari da Rauf Aregbesola na jihar Osun da kuma Ibikunle Amosun najihar Ogun.