Saturday, October 5, 2013

Maniyata 400 sun tsallake rijiya da baya...



Maniyata na sauka daga jirgin a jihar Sakkwato
Da sanyin safiyar yau ne jirgin kamfanin Kabo mai dauke da maniyata akalla dari hudu, daga  jihar Kano ya yi saukar gaggawa a filin tashin jiragen sama na Abubakar na uku dake jihar Sakkwato.

Jirgin kirar boeing 747, ya bar Kano a jiya  Juma'a zuwa kasa mai tsarki, inda babu shiri jirgin ya sauka a jihar na Sakkwato kasancewar fashewar tayoyin jirgin, jim kadan da keta hazo daga filin saukar jirage na Malam Aminu Kano.

A yanzu haka dai, rahotanni sun bayyana cewa maniyatan sun yada zango a wani otal dake jihar ta Sarkin Musulmi.

Allah dai ya tsare ya kuma kiyaye gaba!!!

No comments:

Post a Comment