Alhaji Aliko Dangote |
Za a gina wannan katafaren asibitin ne kusa da asibitin Murtala da ke cikin kwaryar birnin Kano, wanda za a kashe akalla Naira biliyan biyu daga asusun gidauniyar Dangote. Haka kuma za a kira wannan asibiti da suna Mariya Sunusi Dantata.
Asibitin zai hada da dakunan gwaje-gwaje da dakunan yin tiyata goma, da dakunan kula da marasa lafia na musamman wato ICU da kuma dakunan duba marasa lafia, da na likitoci da ma'aikatan jinya da sauransu.
Alhaji Aliko Dangote ya bayyana dalilin gina wannan asibiti inda yace"ba wai dan na yi fice bane amatsayin wanda ya gina asibitin da babu irinsa a fadin Kano ba, illa mun kudiri aniyar ginawa ne domin inganta harkar lafiya da walwalar al'umar Najeriya. Saboda mun san kowanne dan Najeriya na da hakkin samun ingantacciyar lafiya, sannan kuma mu na ganin hakkin mu ne mu hada karfi da karfe wajen amfani da dukiyoyin mu wajen bunkasa cibiyoyin kiwon lafiya da kuma horar da jami'an kiwon lafiya tare da inganta harkar riga-kafi."
Lafiya uwar jiki....babu mai fushi da ke!!!
No comments:
Post a Comment