Friday, October 4, 2013

kakar zawarawan zamfara ta yanke saka...




 

Allah ya amsa addu'ar zawarawan Zamfara domin  kuwa shugaban kungiyar 'yan kasuwa ta jihar Alhaji Ibrahim Sani ya bayyana aniyar kungiyar na daukar nauyin aurar da zawarawa dari ga manema masu sha'awar kari a jihar.

Alhaji Sani, ya shaidawa manema labarai a garin Gusau, inda ya ce sun yi hakan ne domin taimakawa gwamnatin jihar a kokarinta na rage yawan zawarawan,dan haka suka ga bukatar su taimaka dan magance matsalar.

Ya kuma kara da cewa, a yanzu haka an gama shirye-shirye tsaf, kuma nan ba da dadewa ba ba za a tsayar da ranar da ta dace.

Kowa dai ya yi da kyau ...zai ga da kyau..!!!


No comments:

Post a Comment