Wednesday, October 2, 2013

Bikin 'yancin Najeriya na bana bai yi armashi ba.



Obasanjo    da         IBB
 Bikin cikar Najeriya shekara hamsin da uku da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na wannan shekara bai yi armashi ba, a yayin da tsofaffin shuwagabanni  kasa biyar ne su ka yi biris da amsa gayyatar bikin, da aka saba gudanarwa a fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Wadannan shuwagabanni sun hada da Cif Olusegun Obasanjo, da janar Muhammadu Buhari,da Ibrahim Babangida,da Abdusalami Abubakar da kuma Alhaji Shehu Shagari.
Shuwagabannin da suka halarci bikin kuwa su ne janar Yakubu Gawon sai Cif Earnest Shonekan.

Rahotanni sun bayyana cew wannan shi ne  karo na uku da ake gudanar da bikin a fadar gwamnati bayan da bam  ya tashi  a irin wannan bikin da aka gudanar a dandalin Eagle Square da ke garin na Abuja a shekara 2010.

Hausawa dai kan ce abin da babba ya hango ,yaro ko ya hau rimi ba zai hango ba.....!!!

No comments:

Post a Comment