Tuesday, October 22, 2013

An gwabza tsakanin 'ya'yan sabuwa da tsohuwar PDP a Kano





Jam'iyar PDP
                                                       
Wasu 'yan Banga sun apkawa sakatariyar  jam'iyar PDP,tsagin Bamanga Tukur a jihar Kano tare da tarwatsa taron da ake tsaka da yi na kaddamar da kantomar riko na jam'iyar, abinda ya jikkata wasu mahalarta taron. Sakataren jam'iyar ,Ja'afar Sani Bello ya shaidawa manema labarai hakan, Inda ya bayyana cewa 'yan Bangar sun kai musu farmaki , har kuma sun raunata shi da wasu mutum hudu.  

Anata bangaren shugabar mata ta jam'iyar  Hajia Rabi Shehu Sharada ta shaida cewa shedikwatar jam'iyar PDP  da ke babban birnin tarayya Abuja ta umarci manbobin kwamitin  su bayyana a  gabanta a safiyar yau.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Alhaji Musa Daura ya bada tabbacin apkuwar al'amarin, inda yace har an capke wasu mutum hudu da ake zargin suna da hannu aciki..

Masu magana dai kan ce"wuyar aiki ba a fara ba"!!!

No comments:

Post a Comment