Tuesday, October 22, 2013
An gwabza tsakanin 'ya'yan sabuwa da tsohuwar PDP a Kano
Jam'iyar PDP |
Wasu 'yan Banga sun apkawa sakatariyar jam'iyar PDP,tsagin Bamanga Tukur a jihar Kano tare da tarwatsa taron da ake tsaka da yi na kaddamar da kantomar riko na jam'iyar, abinda ya jikkata wasu mahalarta taron. Sakataren jam'iyar ,Ja'afar Sani Bello ya shaidawa manema labarai hakan, Inda ya bayyana cewa 'yan Bangar sun kai musu farmaki , har kuma sun raunata shi da wasu mutum hudu.
Anata bangaren shugabar mata ta jam'iyar Hajia Rabi Shehu Sharada ta shaida cewa shedikwatar jam'iyar PDP da ke babban birnin tarayya Abuja ta umarci manbobin kwamitin su bayyana a gabanta a safiyar yau.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Alhaji Musa Daura ya bada tabbacin apkuwar al'amarin, inda yace har an capke wasu mutum hudu da ake zargin suna da hannu aciki..
Masu magana dai kan ce"wuyar aiki ba a fara ba"!!!
Saturday, October 5, 2013
Maniyata 400 sun tsallake rijiya da baya...
Maniyata na sauka daga jirgin a jihar Sakkwato |
Jirgin kirar boeing 747, ya bar Kano a jiya Juma'a zuwa kasa mai tsarki, inda babu shiri jirgin ya sauka a jihar na Sakkwato kasancewar fashewar tayoyin jirgin, jim kadan da keta hazo daga filin saukar jirage na Malam Aminu Kano.
A yanzu haka dai, rahotanni sun bayyana cewa maniyatan sun yada zango a wani otal dake jihar ta Sarkin Musulmi.
Allah dai ya tsare ya kuma kiyaye gaba!!!
Friday, October 4, 2013
kakar zawarawan zamfara ta yanke saka...
Allah ya amsa addu'ar zawarawan Zamfara domin kuwa shugaban kungiyar 'yan kasuwa ta jihar Alhaji Ibrahim Sani ya bayyana aniyar kungiyar na daukar nauyin aurar da zawarawa dari ga manema masu sha'awar kari a jihar.
Alhaji Sani, ya shaidawa manema labarai a garin Gusau, inda ya ce sun yi hakan ne domin taimakawa gwamnatin jihar a kokarinta na rage yawan zawarawan,dan haka suka ga bukatar su taimaka dan magance matsalar.
Ya kuma kara da cewa, a yanzu haka an gama shirye-shirye tsaf, kuma nan ba da dadewa ba ba za a tsayar da ranar da ta dace.
Kowa dai ya yi da kyau ...zai ga da kyau..!!!
Dangote, gagara badan namiji tsayayyen dan kasuwa...
Alhaji Aliko Dangote |
Za a gina wannan katafaren asibitin ne kusa da asibitin Murtala da ke cikin kwaryar birnin Kano, wanda za a kashe akalla Naira biliyan biyu daga asusun gidauniyar Dangote. Haka kuma za a kira wannan asibiti da suna Mariya Sunusi Dantata.
Asibitin zai hada da dakunan gwaje-gwaje da dakunan yin tiyata goma, da dakunan kula da marasa lafia na musamman wato ICU da kuma dakunan duba marasa lafia, da na likitoci da ma'aikatan jinya da sauransu.
Alhaji Aliko Dangote ya bayyana dalilin gina wannan asibiti inda yace"ba wai dan na yi fice bane amatsayin wanda ya gina asibitin da babu irinsa a fadin Kano ba, illa mun kudiri aniyar ginawa ne domin inganta harkar lafiya da walwalar al'umar Najeriya. Saboda mun san kowanne dan Najeriya na da hakkin samun ingantacciyar lafiya, sannan kuma mu na ganin hakkin mu ne mu hada karfi da karfe wajen amfani da dukiyoyin mu wajen bunkasa cibiyoyin kiwon lafiya da kuma horar da jami'an kiwon lafiya tare da inganta harkar riga-kafi."
Lafiya uwar jiki....babu mai fushi da ke!!!
Wednesday, October 2, 2013
Martanin Kwankwaso a kan taron kasa..
Dr. Rabiu Musa Kwankwaso |
Gwamnan ya bayyana hakan ne, a wata ganawa da manema labarai da ya yi a Kano, a yayin bikin cikar Najeriya hamsin da uku da samun 'yancin kai. Ya kuma shaida cewa taron ba komai zai haifar ba illa fama rauni, maimakon kamo bakin zaren matsalolin da ke addabar kasa, in da ya jaddada cewa al'umar Najeriya babu abin da su ke bukata illa tabbatacciyar wutarlantarki, da kayayyakin more rayuwa.
Gwamna Kwankwaso, ya kuma kara da cewa bayan shekaru hamsin da uku da samun 'yancin kai, har yanzu 'yan Najeriya na fama da yunwa tare da yanke kauna saboda matsalar cin hanci da rashin kyakkyawan shugabanci.
Dakta Kwankwaso, ya kuma shaida cewa matsalar karancin kudi da ke addabar kasa bai shafi jihar Kano ba saboda tsantsaini da hangen nesan shugabanninta.
Ya kuma dora laifin rashin gudanar da zabubbukan kananan hukumomi a jihar Kano, a kan matsalar tsaro, da soke rajistar wasu jam'iyu da aka yi a baya, da kuma sabarta-juyartar siyasa da addabar Najeriya.
Allah dai ya kiyashe mu da taron shan shayi...!!!
Bikin 'yancin Najeriya na bana bai yi armashi ba.
Obasanjo da IBB |
Wadannan shuwagabanni sun hada da Cif Olusegun Obasanjo, da janar Muhammadu Buhari,da Ibrahim Babangida,da Abdusalami Abubakar da kuma Alhaji Shehu Shagari.
Shuwagabannin da suka halarci bikin kuwa su ne janar Yakubu Gawon sai Cif Earnest Shonekan.
Rahotanni sun bayyana cew wannan shi ne karo na uku da ake gudanar da bikin a fadar gwamnati bayan da bam ya tashi a irin wannan bikin da aka gudanar a dandalin Eagle Square da ke garin na Abuja a shekara 2010.
Hausawa dai kan ce abin da babba ya hango ,yaro ko ya hau rimi ba zai hango ba.....!!!
Subscribe to:
Posts (Atom)