Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bayan an rantsar da shi |
A yau ne Babban mai Shari'ah na kasa Mahmud Muhammad ya rantsar da Sabon Zababben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yomi Osibanjo a wani kasaitaccen biki da aka gudanar a dandalin Eagle's Square dake Babban Birnin Tarayya Abuja.
Farfesa Osibanjo ya fara karbar rantsuwar kama aiki yayin da shugaba Buhari ya karbi na sa tare da rakiyar Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan.
Ayayin bikin rantsar da Shugaban Kasa an gudanar da Fareti da sauke tuta da kuma harbin bindiga sau Ashirin da Daya..
Muna Taya Sabon Shugaban Kasa Murna...Allah ya taya shi riko
No comments:
Post a Comment