Tuesday, June 9, 2015

Bukola Saraki Ya zama Shugaban Majalisar Dattawa ta 8


Saraki SNP
Ayayin da ake rantsar da sanata Bukola Saraki
 An zabi Sanata Bukola Saraki a matsayin sabon shugaban Majalisar Dattawa ta Takwas.
Zaman Majalisar na Yau da Akawun Majalisar  Salisu Maikasuwa ya Jagoranta  ya samu halartar Sanatoci 57.
Saraki dake wakiltar Kwara ta tsakiya ya zamo shugaban majalisar dattawa bayan sanata Ahmad Yarima Da Deno Milaye suka gabatar da sunansa amatsayin dan Takara.

Yayin da a hannu guda,Ike Ekweremadu ya sake darewa akan mukaminsada ya rike a majalisa ta 7 amatsayin mataimakin shugaban majalisa.

Ekweremadu ya yi Nasarar kayar da abokin takararsa Sanata Ali Ndume.

Mai Martaba Sarkin Kano da Iyalansa

Mai Martaba  Sarkin Kano da Iyalansa


  A jiya 8 ga watan Yuni, Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya cika Shekara Daya akan Karagamar Mulki.

Sunday, May 31, 2015

Hotunan Liyafar Daren bikin shan rantsuwar Kama aiki


Shugaba Buhari da shuwagabanninAPC sun yi hoto da Matar da ta bada gudummawar Kudi lokacin yakin neman zabe




Shuwagabannin Jam'iyar APC da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari sun dau hoto da matarnan mai siyar da abinci mai shekaru 90 da ta bayar da gudummawar Naira milliyan daya lokacin yakin neman zaben shugaban  kasa. Hajia Fadimatu mai Talle Tara ta samu halartar bikin rantsar da shugaban Kasa

Sabon Dogarin Shugaban Kasa..

Ga fa sabon dogarin shugaban kasa Muhammadu  Buhari, Sunansa Lt.Col . Muhammad Lawal Abubakar dan asalin jihar Kano. Shi ne zai rika tsare lafiyar sabon shugaban Kasa...

Friday, May 29, 2015

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya halarci sallar Juma'a




Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar

 Bayan Liyafar da aka shirya a fadar gwamnati, sabon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci sallar Juma'a a babban masalacin juma'a dake babban birnin tarayya Abuja..
Shugaba Buhari da Mataimakinsa ayayin Liyafar bikin rantsuwar kama aiki





Shugaban kasa Muhammadu Buhari lokacin da zai tafi sallar juma'a

Tsohon Shugaban Kasa Goodluck ya Isa Otueke

Tsohon shugaban kasa Goodluck da maidakinsa Patience
 Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan da mai dakinsa Patience sun isa Mahaifarsa garin Otueke dake jihar Bayelsa,tunda fari sai da ya tsaya a garin Patakwal da Yenagoa kafin isarsa Otueke.

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon shugaban kasar ya samu kyakyawan tarba daga al'umar Otueke.

Iyalan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari







 
 Iyalan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Maidakinsa Aisha da 'ya'yansu aranar bikin rantsuwar Kama aiki

An Rantsar da Muhammadu Buhari amtsayin sabon Shugaban Kasa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bayan an rantsar da shi

A yau ne Babban  mai Shari'ah na kasa  Mahmud Muhammad ya rantsar da Sabon Zababben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yomi Osibanjo a wani kasaitaccen biki da aka gudanar a dandalin Eagle's Square dake Babban Birnin Tarayya Abuja.

Farfesa Osibanjo ya fara karbar rantsuwar kama aiki yayin da shugaba Buhari ya karbi na sa tare da rakiyar Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan.

Ayayin bikin rantsar da Shugaban Kasa an gudanar da Fareti da sauke tuta da kuma harbin bindiga sau Ashirin da Daya..

Muna Taya Sabon Shugaban Kasa Murna...Allah ya taya shi riko