Kungiyar matasa 'yan kasa da shekara 17 na murna bayan da suka karbi kopinsu |
Wannan shi ya bai wa Najeriya dama na cin gasar kopin duniya ta matasa karo na hudu.
Har ila yau,a yau ne ministan wasanni Malam Bolaji Abdullahi zai tarbi kungiyar kwallon kafar, in da ake sa ran zasu dira a filin jirgin sama na Nnamdi azikwe dake babban birnin tarayya Abuja.
A gobe ne kuma, shugaba Goodluck Jonathan zai gana da 'yan wasan a wata gagarumar liyafa da aka shirya musu a fadar shugaban kasa in da ake sa ran masu ruwa da tsaki daga sassa na Najeriya za su halarci liyafar.
No comments:
Post a Comment