Thursday, November 14, 2013

Abu namu...kura da kallabin kitse



https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEiOkPhMSrY8qqV2A8UZFUUFthOk7yl8kQOvChBYZDFFlTEnzrMYEY4WJoiQUxJjITIo9OzDqgt4iL5RYzdcXDt4K8sRdHWGTdVsL9L_aS_A_zwQxAxVCjZ9B1N6WampKrD7zI5RtBnWOhXc/s1600/1395968_10201365071023843_1689450719_n.jpg
Ahmad Adamu, sabon shugaban majalisar matasa kungiyar kasashe renon Ingila
Dan Nigeria, Ahmad Adamu ya dare  kan kujerar shugabancin majalisar matasa ta kungiyar kasashe renon Ingila,in da ya doke abokan takararsa daga kasashe ashirin,bayan zaben da aka yi a jiya,a ,a garin Hambantota na kasar Sri Lanka,a wajen taron kasashe renon Ingila karo na goma sha biyu.

Shi dai Ahmad Adamu, haifaffen jihar Katsina ne, wanda ya yi karatu a Jami'ar Bayero ta Kano, kuma ya ke da digirin-digir-gir a fannin tsimi- da-tanadi(Economics)a jami'ar Newcastle da ke kasar Ingila.

A shekarar 2011watan disamba ne, Ahmad ya kikiri kungiyar ci gaban matasa ta jihar Katsina,kuma shugabanta na farko,wacce kungiyar ke maida hankalinta akan magance rashin aikin yi da kuma tashe-tashen hankula, kuma sakatare ne a kwamitin gyaran tsarin mulki a shekara 2012 ,mai wakiltar Katsina ta tsakiya.

 Ita majalisar renon Ingila tana da mambobi miliyan dubu da dari biyu,sannan dan Nijeriya ne shugabanta, gaba-dai-gaba-dai Najeriya!!

To mu dai a nan sai mu ce Allah ya taya riko!!

No comments:

Post a Comment