|
Sifeton Janar na 'yansandan Najeriya , Muhammad D.Abubakar |
A ranar Asabar din da ta gabata ne mazauna layin Aminu da ke kusa da tsohon cocin YMCA a Tudun Wada Kaduna suka wayi gari cikin tashin hankali saboda samun gawar wani mutum mai suna Musa Aliyu da ke gidan kallo an masa yankar rago.
Mutumin wanda ya jima yana harkar gidan kallon kwallo babu wanda ya san ko su wane ne suka yi masa wannan kisar gilla, illa makwabta sun wayi ne suka tarar da gawarsa a kwance a bakin shagonsa cikin jini.
Wasu da suka ga gawar sun shaida wa manema labarai cewa an sassare shi kafin aka yi masa yankan rago.
Akwai masu zargin wani yaronsa da ke duba masa shago da kashe shi, kasancewar tare suke kwana a shagon. An ce tun daga ranar da abin ya faru babu wanda ya san inda yaron yake.
Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ne ya kawo yaron amma babu wanda ya san daga ina ya kawo shi. Tare kuma da yaron suke kwana a cikin shagon har zuwa lokacin da abin ya faru. Sai dai har yanzu ba a ga yaron ba.
Marigayi Musa ya taba yin aure har yana da da daya, amma wasu sun ce sun rabu da matarsa shi ya sa ya koma kwanan shago a inda yake harkar nuna kwallo.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, DSP Aminu Lawan ya ce sun fara bincike domin gano abin da ya faru a ranar.
Masu iya magana dai kance idan ajali yayi kira ko ba ciwo sai anje...