Thursday, May 5, 2016

A yau ne Tsohon Shugaban Kasa Umaru Musa 'Yar adua shekaru shida da rasuwa


Marigayi Umaru Musa ;Yaradua




Tsohon Shugaban Kasa Umaru Musa 'Yaradua ya rasu a ranar 5 ga watan Mayu Shekara 2010.
Kafin rasuwarsa  shi ne shugaban kasa na 13 a Najeriya inda ya yi shugabanci daga  shekarar 2007 zuwa 2010. Ya kuma taba rike mukamin gwamnan jihar Katsina a shekarar 1999 zuwa 2007.
Allah ya ji kansa ya kyauta makwanci

Wednesday, March 16, 2016

Yarima Sani Bayero ya kusa Angwancewa


Yarima Sani da Aisha
 Yarima Sani Bayero da ne ga marigayi Sarkin Kano Ado Bayero zai angwance a wannan shekara da sahibarsa A'isha
Masoyan sun saki hotunan su a kafar internet domin nuna shirin Auren da ke tafe..

Mahaifin Sani Marigayi Ado Bayero ya kasance Sarkin  Kano daga shekarar 1963 zuwa 6 ga watan Yunin,Shekarar 2014,lokacin da ya koma ga mahaliccinsa kuma Maimartaba Muhammad Sanusi na biyu ya gaji Kawun nasa.

Friday, February 26, 2016

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da tawagarsa sun shiga cikin dakin Ka'aba







A yau ne Sarkin Saudiya Salman Al Saud ya budewa shugaban kasa da ayarinsa cikin dakin Ka'aba amatsayin wata girmamawa ga shugaban.

Sarkin wanda shi ne yake kula da manyan masallatan Makka da Madina, ya bada umarni a budewa shugaba Buhari dakin Ka'aba

Daga cikin wadanda suka shiga dakin mda shugaban kasa sun hada da mai martaba sakin Kano Muhammad Sanusi na biyu da gwamnonin jihohin Zamfara Abdul Aziz Yari da Khashim Shettima na Borno da na jihar Katsina Aminu Masari da Rauf Aregbesola na jihar Osun da kuma Ibikunle Amosun najihar Ogun.



Thursday, February 25, 2016

Gwamna Ganduje ya kai ziyarar aiki kan hanyar AIM




Aranar Litinin din data gabata ne gwamnan jihar kano ya kawo ziyarar aikin hanyar da ake ta AIM dake Farmcenter kusa da Cinimar Marhaba  dake karamar hukumar Tarauni cikin jihar Kano inda gidajen rediyon Cool Da Wazobia suke...
Ga hotuna lokacin da Mahukuntan gidajen rediyon suka karbi bakwancin gwamnan





































..

Tsohon Shugaban kasa Shehu Shagari cika shekaru 91 a duniya


Image result for picture of shehu shagari
A yau ne 25 ga watan Fabrairu tsohon shugaban kasa Shehu Usman Aliyu Shagari ya cika shekaru 91 a duniya. An haife shi aranar 25 ga watan Fabrairu 1925 a kauyen Shagari a Jihar Sakkwato.
Idan za a tuna shi ne shugaban kasa na biyu lokacin mulkin farar hula jamhuriya ta biyu,ya karbi ragamar mulkin kasa  daga 1 ga watan Oktoba 1979 zuwa watan 31 Disamba 1983

Wednesday, February 24, 2016

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar birnin Riyadh inda yake gudanar da Umara a Madina









Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wanda a halin yanzu yake kasar Saudiya domin gudanar da wasu aiyuka, ya bar Babban birnin Riyardh inda ya isa Madina domin gudanar da Umara


Allah yasa karbabbiya ce.........

Mai dakin gwamnan jihar Bauchi ta kawo dauki ga Maralafiya mai fama da cutar sankarar mama



 
Cuta aka ce ba mutuwa ba ..domin kuwa mai dakin gwamnan jihar Bauchi Hajiya Hadiza Muhammad Abubakar ta kawo dauki ga mara lafiyarnan mai fama da da cutar snkarar mama, Sa'adatu Muhamad Giade.

Hotan wannan matashiya ,mai shekaru 19 a duniya kuma marainiya ya karade kafar intanet wadda take a kwance a Asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa  magashiyyan sakamakom cutar sankarar mama.

Acewar sanarwar da jami'in yada labaran mataimakin gwamnan jihar Bauchi Yakubu Adamu ya fitar, Uwargidan gwamnan ta kawo daukin ne ta hannun kungiyarta B-SWEEP dake bada tallafi inda ta bukaci a mika bayanan maralafiyar tare da sanar da mahukuntan asibitin cewa ta dau dawainiyar Sa'adatu Muhammad Giade dan haka a kula da lafiyarta.

Sa'adatu Allah ya kara lafiya.