Marigayi Alhaji Ibrahim BB Farouk |
Marigayi BB Farouk ya kasance mataimakin gwamna alokacin shugabancin Abubakar Rimi,na tsawon shekara daya wanda daga bisani aka tsige shi a shekarar 1980.
Daya daga cikin 'ya'yansa Dr. Farouk BB Farouk ya bada sanarwar rasuwar mahaifinsa ga manema labarai,inda yace mahaifin nasa ya rasu da misalin karfe 12 na rana.
Kafin rasuwarsa marigayin ya sha fama da mutuwar barin rabin jiki har na tsawon shekaru 10.
An dai haifi marigayi BB Farouk a shekara 1932, ya rasu ya bar matan aure biyu da 'ya'ya 32.
Daga cikin 'ya'yansa akwai Dr. Farouk BB Farouk wanda mai baiwa gwamna shawara ne akan karbar baki a fadar gwamnatin Kano.
An dai gudanar da Jana'izarsa a fadar maimartaba sarkin Kano,yayinda aka binne shi a makabartar kofar mazugal.
Allah ya ji kansa ya gafarta masa...
No comments:
Post a Comment