Muhammad Auwal rike da fasfo 2 da takardar fili
Hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa ta'annati wato EFCC ta capke wani Muhammad Auwal da yake gabatar da kansa a matsayin Nasiru Abdulkadir Dantata.
An damke wanda ake zargin ne bayan wani rahoto da aka samu daga sashin kula da filaye na babban birnin tarayya Abuja cewar ya mallaki fili unguwar Maitama dake Abuja dayake mallakin iyalan attajiran nan Dantata.
A yayin bincike an gano cewar wanda ake zargin Muhammad Auwal na da takardun mallakar fili da wasu takardun bogi, haka kuma yana amfani da sunaye biyu da fasfo guda biyu daya da sunan Muhammad Auwal daga jihar Katsina yayin da daya fasfon yake dauke da suna Nasiru Abdulkadir Dantata daga jihar Kano.
Haka kuma an gano mai laifin yana dauke da takardar shaidar dan asalin karamar hukumar Batsari daga jihar Katsina da suna Haruna Lawal Muhammad.
Masu iya magana dai kance rana dubu ta barawo,rana daya jal ta mai kaya!
No comments:
Post a Comment