Tuesday, September 9, 2014

Maniyata daga Kano za su fara tashi a yau

Kasa mai tsarki
 Kimanin maniyata dari biyar da hamsin ne zasu fara tashi zuwa kasa mai tsarki daga nan jihar Kano.
Jami'in hulda da jama'a na hukumar alhazai ta jihar Alhaji Sani Tanko ya shaida hakan ga manema labarai.

Alhaji Tanko yace maniyatan sun fito ne daga kananan hukumomin Wudil, Warawa, Ajingi, Takai, Albasu da kuma Gaya, wadanda za su tashita jirgin kamfanin Max Air.

Jami'in ya kara da cewa daga cikin jiragen da za su yi jigilar maniyatan sun hada da Max Air, Sky Power da kuma jirgin Kabo.

A cewar Tankon, an jawo lokacin fara jigilar alhazan ne daga Laraba zuwa yau Talata sakamakon kammala shirin fara jigilar da kamfanin Max Air ya yi ,inda alhazan za su tashi da karfe goma na daren yau.

Sunday, September 7, 2014

Dubun wani dan damfara ta cika


          Muhammad Auwal rike da fasfo 2 da takardar fili

Hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa ta'annati wato EFCC ta capke wani Muhammad Auwal da yake gabatar da kansa a matsayin Nasiru Abdulkadir Dantata.

An damke wanda ake zargin ne bayan wani rahoto da aka samu daga sashin kula da filaye na babban birnin tarayya Abuja cewar ya mallaki fili unguwar Maitama dake Abuja dayake mallakin iyalan attajiran nan Dantata.
A yayin bincike an gano cewar wanda ake zargin Muhammad Auwal na da takardun mallakar fili da wasu takardun bogi, haka kuma yana amfani da sunaye biyu da fasfo guda biyu daya da sunan Muhammad Auwal daga jihar Katsina yayin da daya fasfon yake dauke da  suna Nasiru Abdulkadir Dantata daga jihar Kano.

Haka kuma an gano mai laifin yana dauke da takardar shaidar dan asalin karamar hukumar Batsari daga jihar Katsina da suna Haruna Lawal Muhammad.

Masu iya magana dai kance rana dubu ta barawo,rana daya jal ta mai kaya!

Bani da shafin facebook ko twitter- inji San Kano


Mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu
Mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu yace ba shi da shafin twitter ko na facebook.

A wata sanarwa da sarkin yayi wanda sabon dan majen Kano Munir Sanusi ya sanyawa hannu, ya ce duk wani shafi na facebook ko twitter da  aka gani da sunan sa ba na shi ba ne.

Dan haka jama'a su lura!

Friday, September 5, 2014

Za a bude makarantu aranar 22 ga watan Satumba



'Yan makaranta

 A yau ne gwamnatin tarayya ta bada umarnin  a bude makarantun firamare da na sakandire a ranar Litinin 22 ga watan Satumbar da muke ciki.

Hakan ya biyo bayan ganawar da aka yi tsakanin Ministan ilimi Mal. Ibrahim Shekarau da kwamishinonin ilimi na jihohin Kasarnan.

Idan za a iya tunawa an dage komawar makarantun zuwa 13 ga watan Oktoba saboda daukar matakai wajen dakile yaduwar cutar Ebola.

Tuesday, September 2, 2014

Jiya ba yau ba...

Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso

 Kun san 'yan jarida muna yawo muka ci karo da wannan hoto,Gwamnan jihar Kano ne lokacin da yake matashinsa ...

Ibrahim BB Farouk ya rasu

bibi farouk
Marigayi Alhaji Ibrahim BB Farouk
 Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Alhaji Ibrahim BB Farouk ya rasu a jiya a wani asibiti mai zaman kansa anan Kano, yana da shekaru 82 a duniya.

Marigayi BB Farouk ya kasance mataimakin gwamna alokacin shugabancin Abubakar Rimi,na tsawon shekara daya wanda daga bisani aka tsige shi  a shekarar 1980.

Daya daga cikin 'ya'yansa Dr. Farouk BB Farouk ya bada sanarwar  rasuwar mahaifinsa ga manema labarai,inda yace mahaifin nasa ya rasu da misalin karfe 12 na rana.

Kafin rasuwarsa marigayin ya sha fama da mutuwar barin rabin jiki har na tsawon shekaru 10.
An dai haifi marigayi BB Farouk a shekara 1932, ya rasu ya bar matan aure biyu da 'ya'ya 32.

 Daga cikin 'ya'yansa akwai  Dr. Farouk BB Farouk wanda mai baiwa gwamna shawara ne akan karbar baki a fadar gwamnatin Kano.

An dai gudanar da Jana'izarsa a fadar maimartaba  sarkin Kano,yayinda aka binne shi a makabartar kofar mazugal.

Allah ya ji kansa ya gafarta masa...