Marigayi Musa Jalingo shi ne sanye da jar shadda |
Rahotanni sun ishe mu cewa daya daga cikin Manyan Furodusoshin Kannywood Musa Muhammad Jalingo ya rasu bayan rashin lafiya da ya sha fama .An yi jana'izarsa tun ranar juma'a 15 ga watan Mayun shekarar 2014 a gidansa dake Sabuwar Gandu cikin birnin Kano.
Kafin rasuwarsa, shine yake da kamfanin shirya fina-finai na Kajal,kuma yakan fito a fina-finan Kannywood amatsayin jarumi. Daga cikin fina-finansa akwai Alawiyya, Ciki daya, Giwar mata, Tsananin so da sauran sauransu.
Ya rasu yabar mace daya da 'ya'ya hudu. Allah ya ji kansa ya gafarta masa...
No comments:
Post a Comment