Friday, May 30, 2014

Saima Muhammad ta zama Amarya!!



Jaruma Saima da Angonta
A gobe Asarbar ne 31 ga watan Mayun shekara 2014 za a daura auren Jarumar kannywood Saima Muhammad ,A unguwar Gama, Brigade cikin birnin Kano da  Misalin Karfe sha daya  na safe.

Idan ba a manta ba Saima na daga cikin  jaruman sahun farko na  Kannywood,daga cikin fina-finan ta akwai Kilu ta ja bau wanda shi ne fim dinta na farko da aka yi a shekara 1996 zuwa 1997 da Kamfani Iyantama Multimedia suka shirya,sai  Iyaka, 'Yanmata,Mumbari, Khushu'i da Zuri'a da sauran makamatansu.

Ko kun san cewa fim din kilu ta ja bau shi ne  fim din da ya fara jan hankalin 'yan mata da samari shiga harkar fim? Saima ta fito da sunan Aina'u a fim din,Kuma fim din ya yi kasuwa...

Muna yi mata fatan alheri...

Thursday, May 29, 2014

A duk sa'ilin da ka yi fushi ka yi asarar farin ciki na sakan 60!!

Abokan aiki kenan daga Tashar mu ta Coolfm da Wazobiafm dake Jihar Legas suke kayatar da masu karanta wannan shafi, Shugaban Rukunin Tashoshin Amin Mousalli shi ne akan tebir...

Ka ziyarce mu idan har ka baiwa farin ciki muhimmanci!!!

Speta janar ya kusa zama angon karni...




M.D Abubakar da Zahra
Kun san mu ba ma rabo da tsegumi, rahotanni sun ishe mu cewa speta janar din 'yan sandan kasarnan Muhammad Dikko Abubakar ya ku san zama angon karni.

Idan ba ku manta ba Speta janar din ya sake aure a watan Satumbar shekarar 2013 bayan mutuwar matarsa Maryam Abubakar a watan Jinairun shekara 2012.

M.D Abubakar ya auri Zahra Bunu, 'ya ga tsohon jakadan kasar Faransa a shekara 1999 Alh Bunu Sheriff Musa.

Speta janar mai shekaru 54 da Amaryarsa Zahra mai shekaru 36 zasu dansu na fari nan ba da dadewa ba.

Muna addu'ar Allah ya raba lafiya.... 

Wednesday, May 28, 2014

Sarkin Gombe ya kwanta dama...



Marigayi Sarkin Gombe Alh Dr.Shehu Abubakar
 A yammacin jiya ne  muka samu rahoton rasuwar sarkinGombe Alh Dr.Shehu Abubakar,wanda ya rasu a jiya a wani asibiti dake kasar Ingila, bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Sakataren gwamnatin jihar Gombe Abubakar Bage ya bada tabbacin rasuwar acikin wata sanarwa da ya fitar.

Rahotanni sun bayyana cewa a yau ne ake sa ran dawo da gawar marigayin gida Najeriya domin sitirta ta.

Kafin rasuwarsa,Sarki Gomben shugaban majalisar  saurautun gargajiya  na jihar Gombe tun shekarar 1984.

Allah ya jikansa ya gafarta masa..

Monday, May 26, 2014

Abin ya zo...in ji mai tsoron wanka!


Jaruma Hadiza Gabon
Rahotanni sun ishe mu cewa shahararriyar jarumar Kannywood Hadiza Aliyu wacce aka fi sani da Hadiza Gabon za ta shiga daga ciki...Ana sa ran daura auren a ranar Juma'a 30 ga watan da muke ciki.

Jaruma Hadiza Gabon  ta  shiga  harkar fim a shekarar 2009,daga cikin fina-finanta akwai 'Yar maye, Zaman Take, Badi ba rai, Basaja,Daga ni sai ke, Babbar Yarinya da sauran makamantansu.

Mu na yiwa amaryar nan da kwana uku fatan alheri!!

Tuesday, May 20, 2014

Furodusa Musa Jalingo Ya kwanta dama



Photo: Furodusa Musa Jalingo Ya Rasu

Allah yayi wa Musa Jalingo rasuwa yau 17th May 2014 Musa jalingo dai yana daya daga cikin manyan furodusoshin masana'antar fim, kuma jarumi.
Za a yi Jana'izarsa a gidansa dake Sabuwar Gandu. Allah ya gafarta masa yasa ya huta amin! Shine kuma mai kamfanin Kajal Films Production.

Musa Jalingo shine sanye da jar shadda daga dama.
Marigayi Musa Jalingo shi ne sanye da jar shadda


Rahotanni sun ishe  mu cewa daya daga cikin Manyan Furodusoshin Kannywood Musa Muhammad Jalingo ya rasu bayan rashin lafiya da ya sha fama .An yi jana'izarsa tun ranar juma'a 15 ga watan Mayun shekarar 2014 a gidansa dake Sabuwar Gandu cikin birnin Kano.

Kafin rasuwarsa, shine yake da kamfanin shirya fina-finai na Kajal,kuma yakan fito a fina-finan Kannywood amatsayin jarumi. Daga cikin fina-finansa akwai Alawiyya, Ciki daya, Giwar mata, Tsananin so da sauran sauransu.

Ya rasu yabar mace daya da 'ya'ya hudu. Allah ya ji kansa ya gafarta masa... 








Wednesday, May 14, 2014

Bikin ranar yara....

Ina yara Manyan gobe? ga ranar ku nan...Iyaye ku kai 'ya'yan ku kada ku bari a baku labari

Maryam Mushaqqa ta koma dakinta...


Jaruma Maryam

Jarumar Duniyar Kannywood Maryam ta koma dakinta...Rahotanni sun bayyana cewa jarumar ta koma harkar fim bayan mutuwar auren...saidai kuma da yake zaman bai kare ba maigidan ta ya yi bikon matarsa kuma har ta koma dakinta wajen mijinta da 'ya'yanta hudu a kasar Kamaru
.
Daya daga cikin fina-finan ta shi ne Sarmadam wanda suka yi ita da marigayi Ahmad S.Nuhu.

Mu anan mu na yi mata fatan alheri kuma Allah yasa mutu ka raba..

Monday, May 5, 2014

Allah sarki...Akwana a tashi...

Marigayi Umaru Musa Yar'adua

A rana irin ta yau 5 ga watan Mayu shekara 2010 shugaban kasa Umaru Musa Yar'adua ya kwanta dama sakamakon rashin lafiya da ya sha fama.

Kafin rasuwarsa,shi ne shugaban kasar Najeriya  na 13,Ya kuma rike mukamin gwamnan jihar Katsina daga  29 ga watan Mayu shekara 1999 zuwa 29 ga watan Mayu shekara 2007.

Shi ne ya lashe zaben Shugaban kasa mai cike- da kace-nace karkashin Jam'iyar PDP da aka gudanar a 21 ga watan Afrilu kuma aka rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu shekara 2007
.
A Shekara 2009 Ya bar gida Najeriya zuwa Kasar Saudiya domin duba lafiyarsa abisa matsalar da ta shafi Koda.
A ranar 24 ga watan Fabrairu 2010 ya dawo gida Najeriya bayan ya sha fama da jinya ,inda ya rasu a ranar 5 ga watan Mayu,A ka kuma binne shi aranar 6 ga watan Mayu  a Unguwar Yar'adua.
Ya rasu ya bar Mata daya da 'ya'ya takwas...

 Yau shekaru hudu kenan da ya bar duniya...Allah ya jikansa ya gafarta masa... 

Friday, May 2, 2014

Sisi wazobia na gayyatarku!!


Za a gudanar da bikin a St Charles Hall titin zungeru dake Sabon gari ,Kano .A ranar Asabar 10 ga watan Mayu,kudin shiga 1500 ga ma'aurata kuma 2500....