Monday, February 3, 2014

Hira da Fati Bararoji


Hira da Fati
Shahararriyar 'yan wasan fim din hausa Fati Baffa Fagge wacce aka fi sani da Fati Bararoji ta leko zauren mu ga kuma yadda hirar mu ta kasance da ita...

An haife ta a dandali cikin Fagge,ta yi karatun firamare a Festival firamare ,ta je karamar sakandire  ta jahun ta kuma karasa a babbar sakandire dake Garki. Ta kuma yi Karamar Diploma da Babbar Diploma  a  Kwalejin ilimi wato FCE in da ta karanci  Akanta da binciken kudi wato Accounting and Auditing
 daga nan ta shiga harkar fim.

Abin da ya ja hankalin ta, ta shiga Fim...
Sakon Fadakarwa da ke kunshe cikin  fina-finan Hausa sune suka ja hankalinta,inda ta bada misali da fim din Zarge(Nura Hussain da Fati Muhammad)shi ne fim din farko da ta kalla kuma sakwannin cikin fim din suka birgeta,ya bata tausayi har ta yi kuka daga nan ne ta ga ita ma tana da gudummawar da take son isarwa ga alumma.

Ta shaida mana cewa ta dau akalla shekara goma sha biyu a duniyar Fina-finan Hausa na Kannywood inda ta fara da fim din Mashi a wanda a wannan fim din ne ta samu lakanin Fati Bararoji..Daga cikin fina-finan ta akwai Tubali, Sunduki, Kamala , Haraba, Tutar so da sauransu.

Nasarori...
Ta bayyana su kamar farin jini, Nasibi, Alheri da daukaka da hanyar biyan bukatun ta na yau da kullum duk ta samu ne ta dalilin  fina-finan Hausa, kuma ta yi wa Allah godiya da arzikin da ya yi mata.

Kalubale...
Bai wuce na kiran matan fina-finan Hausa karuwai sun ki aure ba..ta shaida cewa babu macen da ta ke kin aure sai dai in lokaci bai yi ba.

 Baya ga harkar fim...
Tana saye da siyarwa na kayan mata da maza kuma tana da wajen gyaran gashi na mata (saloon) nan cikin Fagge.
Aminu Momoh, Nadiya da Fati Bararoji

No comments:

Post a Comment