Friday, February 28, 2014

Duk mai rai mamaci ne





Marigayiya Rabi Mustapha
Shahararriyar mawakiyar fina-finan Kannywood Rabi Mustapha ta rasu.
Ta rasu aranar larabar da ta gabata  26 ga watan da muke ciki bayan 'yar gajeriyar rashin lafia.

Kafin rasuwarta, tana daga cikin mawakan farko a duniyar Kannywood,kuma daga bisani ta fara shirin girke-girken mu a tashar farin wata.

Ta rasu ta bar da daya da mahaifiyarta.

Daga cikin wakokin ta akwai ki yarda dani, Layyo ne
Allah ya jikanta ya sa ta huta,mu kuma ya kyautata namu zuwan.

Sunday, February 9, 2014

Kunsan ta haihu?


Mai jego Rukayya Dawayya da jaririnta Umar
Jarumar Kannywood Rukayya Dawayya da tayi aure a ranar 6 ga watan yulin shekara 2012 ta haifi danta Umar Arfat Adamu Teku a kasar Saudiyya.
Mu na sanar da masoyanta da ku sha kurumin ku domin kuwa tana tafe zuwa gida Najeriya domin bikin suna.. Allah ya raya ya kuma dayyaba!
Umar Arfat 

Jiya ba yau ba...

Wasu  Jarumai mata na Kannywood da suka bace a duniyar fina-finan Hausa da muka tsinkaya a bikin jaruma Rukayya Dawayya da aka gudanar shekarru biyu da suka gabata..
Rasheeda, Amarya da Saima

Maryam Ahmed da Amarya

Sadiya Gyale da Amarya Rukayya
Zainab Idris

Abida da Muheebah

Ina masoyan zamani?


Ina masoyan zamani ,gidan rediyon coolwazobia tare da hadin gwiwar otal din K-suits zasu gudanar da ranar masoya ,ranar Juma'a 14 ga watan fabarairu.

Maza a nemi tikitin shiga a gidan rediyon na Coolwazobia!!

Hoton mu na yau...


Shehu Jibrin (Golobo)

Marigayi Shehu Jibrin da aka fi sani da golobo,wanda ya rasu a watan jiya,idan baku manta ba jarumi ne a wassanin barkwanci na gidan talabijin NTA sakwato kafin ya koma duniyar Fina-finai na Kannywood.
 Allah yaji kansa da rahama. 

A tare mu...a shirin lafiyar Iyali!




Lafiyayyun hakwara
Ko kasan yadda hakoran bakin dan adam suke, tsaftarsu da riga-kafi? A tare mu karfe uku da rabi na yammacin yau a tashar wazobia fm 95.1 domin jin shirin lafiyar Iyali....ko kuma a lalube mu a shafin internet a www.wazobiafm.com domin sauraron shirin. Sai mun ga sakwanninku!!

Monday, February 3, 2014

Hira da Fati Bararoji


Hira da Fati
Shahararriyar 'yan wasan fim din hausa Fati Baffa Fagge wacce aka fi sani da Fati Bararoji ta leko zauren mu ga kuma yadda hirar mu ta kasance da ita...

An haife ta a dandali cikin Fagge,ta yi karatun firamare a Festival firamare ,ta je karamar sakandire  ta jahun ta kuma karasa a babbar sakandire dake Garki. Ta kuma yi Karamar Diploma da Babbar Diploma  a  Kwalejin ilimi wato FCE in da ta karanci  Akanta da binciken kudi wato Accounting and Auditing
 daga nan ta shiga harkar fim.

Abin da ya ja hankalin ta, ta shiga Fim...
Sakon Fadakarwa da ke kunshe cikin  fina-finan Hausa sune suka ja hankalinta,inda ta bada misali da fim din Zarge(Nura Hussain da Fati Muhammad)shi ne fim din farko da ta kalla kuma sakwannin cikin fim din suka birgeta,ya bata tausayi har ta yi kuka daga nan ne ta ga ita ma tana da gudummawar da take son isarwa ga alumma.

Ta shaida mana cewa ta dau akalla shekara goma sha biyu a duniyar Fina-finan Hausa na Kannywood inda ta fara da fim din Mashi a wanda a wannan fim din ne ta samu lakanin Fati Bararoji..Daga cikin fina-finan ta akwai Tubali, Sunduki, Kamala , Haraba, Tutar so da sauransu.

Nasarori...
Ta bayyana su kamar farin jini, Nasibi, Alheri da daukaka da hanyar biyan bukatun ta na yau da kullum duk ta samu ne ta dalilin  fina-finan Hausa, kuma ta yi wa Allah godiya da arzikin da ya yi mata.

Kalubale...
Bai wuce na kiran matan fina-finan Hausa karuwai sun ki aure ba..ta shaida cewa babu macen da ta ke kin aure sai dai in lokaci bai yi ba.

 Baya ga harkar fim...
Tana saye da siyarwa na kayan mata da maza kuma tana da wajen gyaran gashi na mata (saloon) nan cikin Fagge.
Aminu Momoh, Nadiya da Fati Bararoji

Mawakiya Fa'iza Badawa


Mawakiya Faiza Badawa
Ga wadan da basu san ta ba su ke jin wakokin ta,to yau zauren mu ya yi katarin ganawa da ita ga kuma tsarabarta a takaice:

An haifi matashiyar  mawakiya Fa'iza  a unguwar 'Yankaba a cikin birnin Kano Shekaru 23 da suka gabata.

Ta fara waka a shekara 2004 da wakokin yabo, wacce wakar Isra'i ta kasance ta farko..Daga cikin wakokin yabon akwai Kano ta Manzon Allah, Buri na zuciya , Ya rasulillahi, Agaji da sauransu.

Haka kuma mawakiyar ta kuma yi fice a wakokin fina-finan Hausa na Kannywood inda tace bata ma san adadin su ba, daga cikin wakokin fim din Kannywood akwai Daren alkhairi, Babbar rabo, Babban yayana, Tunziri, Zaman idda da sauransu.

 Haka kuma mawakiyar ita ce ta rere wakar Radiyo wazobia a kano ba a samu kamar ki ba... 

Saturday, February 1, 2014

babbar harka...

8
Jamil Abubakar A tsakiya

Yau shafin na mu tsegumin babban dan Speta Janar 'yan sandan kasarnan Muhammad  D.Abubakar, Jamil Abubakar  za mu guntsa muku.
Jamil,ya yi karatu a jami'ar Kingston  akan harkokin fasahar sadarwa ,a yanzu haka matukin jirgin sama ne ,kuma yana da wajen koyon ilimin fasahar sadarwa kyauta a jihar zamfara. A ranar larabar da ta gabata ne ya kara shekara daya akan shekarunsa inda kuma ya ziyarci gidan marayu domin nuna farin cikinsa game da wannan rana.ga kuma irin babbar harkar ...
9

01

5


22